Labaran wasanni

Zan samar da sauyi a Manchester United – Shaw

Dan wasan baya na Ingila Luke Shaw ya ce yana da yakinin cewa zai samar da kwakkwaran sauyi ga kungiyar kwallon kafa ta Manchester United bayan sanya hannu kan sabon shekaru 5 yau Alhamis.


Shaw mai shekaru 23 na sabunta kwantiragin nasa ne kan na shekaru 4 da ya karar tun bayan sauya shekarsa daga Southampton lokacin da United din ta saye shi a matsayin matashin dan wasa mafi tsada a duniya.
Shaw wanda ya shafe kusan shekaru 3 ba a jin duriyarsa tun bayan karayar da ya samu a kafarsa a shekarar 2015 dalilin da ya tilasta masa bai wa Tamaula baya, koda dai matakin ya haddasawa Jose Mourinho caccaka daga masoyan matashin dan wasan.
A cewar Shaw ya yi atisaye tukuru don ganin ya dawo da hazakarsa bayan shafe lokaci yana jinya kuma ya yi imanin cewa a shirye ya ke ya sanya Club din alfahari.
Yanzu haka dai Manchester United wadda ke matsayin ta 8 a teburin firimiya akwai tazarar maki 7 tsakaninta da manyan kungiyoyin Firimiya da suka hadar da Manchester City da Chelsea da kuma Liverpool.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button