ABIN MAMAKI

Zan Fallasa Asirin Kwankwasiyya – Naziru Sarkin Waƙa

Zan Fallasa Asirin Kwankwasiyya – Naziru Sarkin Waƙa
A wani rahoto da mu ka samu daga majiya mai karfi, an jiyo sarkin wakar sarkin kano Naziru M Ahmad ya na ikirarin fasa KWAN  kungiyar kwankwasiyya muddin dai ba su daina zaginsa ba.
Naziru ya fadi cewa
   “A saboda na goyi bayan malam isah pantami wai yau ni Naziru Sarkin Waka yan kwankwasiyya za su rika zagi da furta kalaman batanci da yarfe da kuma kage a kaina.
Da dama daga mutane sun ga inda na yi rubuce,rubuce a shafina kan yabon malam pantami amma sai yan kwankwasiyya su ka shiga su ke zagina da cin zarafina. NAZIRU ya ce.
Karara kenan sun tabbatar da kungiyar kwankwasiyyya a matsayin kungiyar rashin da’a da tarbiyya. kungiyar da ba a ganin girma da mutuncin kowa. kungiyar da duk yadda ka kai a cikinta abu ne mai sauki a ci zarafinka a aibata ka saboda ka fadi wani ra’ayi ko fahimta da ta saba da ta yan kungiyar.
wannan kuma shi ne tsarin da aka dora matasanmu akai ka da su ga girman kowa ka da su mutunta kowa su zama fitsararru kangararru kuma zagi da yarfe da kage da cin zarafin masu mutunci ba komai ba ne a wurinsu.
yanzu saboda Allah in ba rashin kunya ba, wai yau ni NAZIRU za a duba a kwankwasiyya a zaga a keta alfarmata, ai na fi karfin haka a kwankwasiyya da ace da girma da arziki da kuma ganin mutuncin mutane ga yayan kungiyar.
saboda haka daga yau ni dai na ja layi matukar aka cigaba da zagina da ci min fuska a kwankwasiyya to ba tare da bata lokaci ba zan fasa tula, zan tona abubuwa da dama wadanda mutane ba su sani ba domin su sani in ya so kungiyar ma ta watse gaba daya kowa ma ya huta. 
Wannan su ne kadan daga cikin kalaman da majiyarmu ta jiyo sarkin wakar ya na furtawa kan kwankwASIYYA da yan kwankwasiyyar. Kuma mun ziyarci shafin nazir a Istagram mun ga yadda yan kwankwasiyyar su ke zaginsa kaca-kaca.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button