Abin Alajabi

ZAKI: Yadda ta kaya da Zakin da ya balle a Kano

Yadda ta kaya da Zakin da ya balle a Kano
Hukumomi a Kano sun ce bayan dogon artabu da aka sha, a karshe dai an samu rikakken zakin da ya tsere daga gidansa a gidan namun daji na jahar Kano (wato gidan Zoo).
Shugaban hukumar gidan namun dajin ya ce bayan da allurar kashe jiki da aka yi masa ta ki yin aiki aka kuma kasa mayar da shi dakin nasa, sai aka yi masa dabara wajen daure akuya a cikin dakin inda bayan ya hangota, sai ya koma ciki.
“Akwai wani mai kula da shi da ke ba shi abinci mai suna Musbahu, wanda har yana iya magana da shi ta hanyar alamu, to da shi ne aka samu shawo kan zakin wajen nuna masa akuyar da aka ajiye a dakin nasa, hakan kuma ta sa nan da nan zakin ya shige ciki sai aka rufe,” in ji shugaban Gidan Zoo.
Tun a ranar Asabar ne rikakken zakin ya tsere daga gidansa, amma hukumomin kula da gidan adana namun dajin sun ce sun dauki matakai ta yadda ba zai iya shiga gari ba.
A ranar Lahadi ne shugaban Gidan Zoo din Sa’idu Gwadabe Gwarzo ya ce Zakin ya ci awaki guda uku daga nan kuma ya shiga bangaren jimina ya yi barna.
Ya ce duk da an ga inda zakin ya shiga amma ba a kama shi domin mayar da shi gidansa ba, saboda “magungunan da aka ba shi don galabaitar da shi ba su yi masa aiki ba,”
Tun da fari hukumomi sun ce idan dai har aka gagara mayar da zakin gidansa, to za a iya dauki rayuwarsa wanda shi ne mataki na karshe, kamar yadda kungiyar kula da dabbobi ta duniya ta bayar da umurni a cewar Sa’idu Gwarzo.
Akwai kwararru da suka je Kano daga Abuja domin yi wa zakin allurar da za ta galabaitar da shi don kama shi a mayar da shi kejinsa.
An toshe dukkanin kofofin Gidan Zoo tsawon kwanaki biyu don hana zakin iya fita ya shiga gari.
Sannan ma’aikatan Gidan Zoo din sun yi ta yawo da wasu motoci na aiki a cikin gidan suna zagaye don neman lunkun da zakin ya shige.
Hukumomi sun yi ta kira ga al’ummar Kano musamman wadanda ke makwabtaka da gidan adana namun dajin su kwantar da hankalinsu domin an dauki matakai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button