Labaran siyasa

Zaben 2019: PDP Ta Nemi Ayi Muhawara Tsakanin Buhari Da AtikuJam’iyyar adawa ta PDP ta kalubalancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya shirya fuskantar muhawara tsakaninsa da Atiku, akan lamurran da suka shafi inganta rayuwar ‘yan kasa. 

Jam’iyyar ta bayyana wannan matsaya nata ne a jiya, a wata takardar manema labarai da mai magana da yawun jam’iyyar, Kola Ologbondiyan ya sake. Inda ya ce, Shugaba Buhari na iya zabar muhallin da yake muradi domin a yi wannan muhawara, wanda kuma kwamitin lura mai zaman kansa zai lura da shi. 

Jam’iyyar ta yi ikirarin cewa Muhammadu Buhari na tsoron yin irin wannan muhawara da Atiku, wacce za a mayar da hankali wurin tattauna batutuwan da suka shafi inganta rayukan ‘yan Nijeriya. 

Sanarwar ta ce; “Dole ne Buhari ya fuskanci Atiku, domin ‘yan Nijeriya ba shirye suke su aminta da wani wakili ba, ko da kuwa wanene. Idan har shugaban kasa ba zai iya fuskantar abokin karawarsa ba, to ta ya zai iya karawa da shugabanni daga kasashen waje?

yanzu dai ’yan Nijeriya na iya ganin dalilin da ya sa Nijeriya ba ta ci gaba a wadannan shekaru uku da rabi. 
Shugaban kasa Buhari kawai ya shiryawa wannan muhawara domin da ita ne za a iya tantance irin ayyukan da gwamnatinsa ta yi a tsawon zamaninta.” inji shi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button