Labaran siyasa

Za`A Fara Shan Wutar Awa 24 Idan Har Buhari Ya Zarce

Za’a fara shan wutar awa 24 idan har Buhari ya zarce

Amaechi yace gwamnatin Buhari ta ciri tuta wajen habbaka lamarin tsaro, gine ginen hanyoyi, yaki da rashawa, inganta harkar

noma da kuma harkar abinda ya shafi sufuri, haka zalika Buhari bai yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da yan bindigan Fulani makiyaya.

“A yanzu haka an samu cigaba adadin wutar da ake samarwa a Najeriya, daga mega watta dubu uku, zuwa mega watta dubu bakwai,

amma megawatt dubu biyar kawai zamu iya rarrabawa saboda akwai wasu kayan aikin da suka lalace, amma a hankali muna gyarasu.

“Duk wanda yace ma’aikatar ayyuka ba ta aiki bai mata adalci ba, saboda akwai hanyar Bonny wanda aka watsar da ita tun bayan Obasanjo, amma zuwanmu sai gashi mun dauki gabarar gudanar da aikin duk da cewa kudin aikin ya karu.” Inji Amaechi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button