Labarai

Za-mu Soke Lefe Da Kudin Na Gani Ina So a Harakar Aure.

SANUSI LAMIDO:
.
Za-mu Soke Lefe Da Kudin Na Gani Ina So a Harakar Aure.
.
Mai martaba sarkin Kano Muhammad Sanusi na II ya bayyana cewa: idan samari za su yarda, a soke lefe a hidimar aure, sannan a zaftare kudin sadaki ya dawo naira 10,000, kacal akan ko wace mace. 
Sannan da wasu kudaden gaisuwa da nagani ina so da ake kaiwa iyaye. “Amma kuma idan an tashi kawo matar, za’a kawo ta da yar tabarma, da bargo, da bokiti guda, da butar alwala, sannan babu maganar kayan gara da kujeru.
To a shirye muke da mu kafa dokar hana lefe da biyan sadaki mai yawa da sauran bidi’o’i, akwai iyayen yara mata da dama wadanda suka goyi bayan mu kafa wannan doka amma matsalar daga bangaren samari take. 
Saboda haka idan samari za su yarda to za-mu kafa wannan doka. “In ji sarkin Kano Sanusi Lamido.” 
Kunji fa menene ra’ayinku shin yan mata da samari kuna goyon bayan hakan? Bayyana ra’ayoyinku yana da matukar muhimmanci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button