Labarai

Yunwa: Yara Miliyan 2.5 Ke Fama Da Cutar Tamowa A Nijeriya

Wani jami’in Nijeriya ya fada a ranar Litinin cewa, kimanin yara kanana ‘yan kasa da shekaru biyar milyan 2.5 ne suke fama da cutar rashin samun isasshen abinci mai gina jiki a kasar nan.
Ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Udoma Udoma ya ce, hatta wadanda ma ba wadannan din ba, sukan tashi ne da rashin ingantacciyar kwakwalwa, tsamurewa, tsumburewa da kuma rashin kuzari a jiki, wanda hakan ke shafan kokarin su a makaranta a bayan sun girma.
Ministan ya bayar da wadannan misalan marasa dadin ji ne a wajen kaddamar da bukin makon cin abinci mai inganta jiki na shekarar 2018. Da yake jawabin bude taron a Abuja, ranar Litinin, Ministan wanda babban Sakataren ma’aikatarsa, S.O.S Odewale, ya wakilce shi, ya bayyana wannan bayanin a matsayin abin damuwa matuka. Mista Udoma ya bayyana cewa, an zabi taken makon na wannan shekaran ne domin ya janwo hankalin wadanda abin ya shafa a kan su gaggauta daukan matakan da suka dace.
“Makon cin abinci mai gina jiki wanda ake yin sa a duk shekara yana taimakawa wajen wayar da kai kan mahimmancin cin abinci mai gina jiki musamman ga kananan yara da kuma mahimmancin sa wajen samar da ci gaba da habakan tattalin arzikin kasa.
“Sakamakon da ake samu wajen irin wannan taron shi ne, zaburantar da bin hanyoyin magance matsalar rashin samar da abinci mai gina jiki, da akasin hakan wanda yake nakasu ne ga ci gaban kasa da kuma ma a wasu lokutan yakan kara wa kasafin kudi nauyi wajen nemo hanyoyin magance rashin abincin mai gina jiki.
“A kan hakan ne muka kebance wani sashe a kasafin kudi domin samar da abinci mai gina jiki. Mun kuma bayar da shawarar ya kamata dukkanin sassan ma’aikatu da hukumomin gwamnati su ma ya kamata su yi hakan,” in ji Ministan.
Wata kwararriya a kan abinci mai gina jiki, Bunmi Lawan, a jawabin ta, ta bayyana hadurran da ke tatter da rashin cin abinci mai gina jiki musamman ga yara kanana a kwanakin su dubu da haihuwa a wannan duniyar.
Ta nemi gwamnati da ta zuba jari mai yawa a kan samar da abinci mai gina jiki, ”especially folic acid fortification,” wanda ta kwatanta da mahimmin abin da jiki ke bukata domin gina ingantacciyar kwakwalwa da kasusuwan gadon baya. Ta kuma yi kira ga kungiyoyi, bankuna da kamfanonin sadarwa da su taimaka wajen kara wayar da kai a kan hadurran da ke tattare da rashin cin abinci mai gina jiki. Lilian Ajah-mong, jami’in sadarwa na daya daga cikin kungiyoyin da suka shirya taron mai suna, Civil Societies Scaling-Up Nutrition in Nigeria, CS-SUNN, ya bayyana dalilan da suka sanya cin abinci mai gina jiki ya zama tilas a rayuwa. Baya ga ganawa da manema labarai na kwana guda din, za a kwashe tsawon makon ne wajen ayyukan wayar da kai kan mahimmancin cin abincin mai gina jiki a Masallatai da Coci-Coci da kuma shirya taruka a wuraren da mutane suke taruwa.

anda ta kwatanta da mahimmin abin da jiki ke bukata domin gina ingantacciyar kwakwalwa da kasusuwan gadon baya. Ta kuma yi kira ga kungiyoyi, bankuna da kamfanonin sadarwa da su taimaka wajen kara wayar da kai a kan hadurran da ke tattare da rashin cin abinci mai gina jiki. Lilian Ajah-mong, jami’in sadarwa na daya daga cikin kungiyoyin da suka shirya taron mai suna, Civil Societies Scaling-Up Nutrition in Nigeria, CS-SUNN, ya bayyana dalilan da suka sanya cin abinci mai gina jiki ya zama tilas a rayuwa. Baya ga ganawa da manema labarai na kwana guda din, za a kwashe tsawon makon ne wajen ayyukan wayar da kai kan mahimmancin cin abincin mai gina jiki a Masallatai da Coci-Coci da kuma shirya taruka a wuraren da mutane suke taruwa.

Read More at: https://leadershipayau.com/2018/11/21/yunwa-yara-miliyan-2-5-ke-fama-da-cutar-tamowa-a-nijeriya/

Wani jami’in Nijeriya ya fada a ranar Litinin cewa, kimanin yara kanana ‘yan kasa da shekaru biyar milyan 2.5 ne suke fama da cutar rashin samun isasshen abinci mai gina jiki a kasar nan. Ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Udoma Udoma ya ce, hatta wadanda ma ba wadannan din ba, sukan tashi ne da rashin ingantacciyar kwakwalwa, tsamurewa, tsumburewa da kuma rashin kuzari a jiki, wanda hakan ke shafan kokarin su a makaranta a bayan sun girma. Ministan ya bayar da wadannan misalan marasa dadin ji ne a wajen kaddamar da bukin makon cin abinci mai inganta jiki na shekarar 2018. Da yake jawabin bude taron a Abuja, ranar Litinin, Ministan wanda babban Sakataren ma’aikatarsa, S.O.S Odewale, ya wakilce shi, ya bayyana wannan bayanin a matsayin abin damuwa matuka. Mista Udoma ya bayyana cewa, an zabi taken makon na wannan shekaran ne domin ya janwo hankalin wadanda abin ya shafa a kan su gaggauta daukan matakan da suka dace. “Makon cin abinci mai gina jiki wanda ake yin sa a duk shekara yana taimakawa wajen wayar da kai kan mahimmancin cin abinci mai gina jiki musamman ga kananan yara da kuma mahimmancin sa wajen samar da ci gaba da habakan tattalin arzikin kasa. “Sakamakon da ake samu wajen irin wannan taron shi ne, zaburantar da bin hanyoyin magance matsalar rashin samar da abinci mai gina jiki, da akasin hakan wanda yake nakasu ne ga ci gaban kasa da kuma ma a wasu lokutan yakan kara wa kasafin kudi nauyi wajen nemo hanyoyin magance rashin abincin mai gina jiki. “A kan hakan ne muka kebance wani sashe a kasafin kudi domin samar da abinci mai gina jiki. Mun kuma bayar da shawarar ya kamata dukkanin sassan ma’aikatu da hukumomin gwamnati su ma ya kamata su yi hakan,” in ji Ministan. Wata kwararriya a kan abinci mai gina jiki, Bunmi Lawan, a jawabin ta, ta bayyana hadurran da ke tatter da rashin cin abinci mai gina jiki musamman ga yara kanana a kwanakin su dubu da haihuwa a wannan duniyar. Ta nemi gwamnati da ta zuba jari mai yawa a kan samar da abinci mai gina jiki, ”especially folic acid fortification,” wanda ta kwatanta da mahimmin abin da jiki ke bukata domin gina ingantacciyar kwakwalwa da kasusuwan gadon baya. Ta kuma yi kira ga kungiyoyi, bankuna da kamfanonin sadarwa da su taimaka wajen kara wayar da kai a kan hadurran da ke tattare da rashin cin abinci mai gina jiki. Lilian Ajah-mong, jami’in sadarwa na daya daga cikin kungiyoyin da suka shirya taron mai suna, Civil Societies Scaling-Up Nutrition in Nigeria, CS-SUNN, ya bayyana dalilan da suka sanya cin abinci mai gina jiki ya zama tilas a rayuwa. Baya ga ganawa da manema labarai na kwana guda din, za a kwashe tsawon makon ne wajen ayyukan wayar da kai kan mahimmancin cin abincin mai gina jiki a Masallatai da Coci-Coci da kuma shirya taruka a wuraren da mutane suke taruwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button