Labaran siyasa

Yanzu Yanzu: An tsaurara matakan tsaro a Ado-Ekiti yayinda ake rantsar da Fayemi

An tsaurara matakan tsaro a Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti yayinda ake rantsar da zababben gwamnan jihar, Dr Kayode Fayemi a matsayin gwamnan jihar.
A tsakar daren jiya Litinin, 15 ga watan Oktoba wa’adin mulki tsohon gwamnan jihar Ayodele Fayose ya cika.

Babban alkalin alkalai na jihar Ekiti, Justis Ayodeji Daramola ne zai rantsar da Fayemi tare da mataimakinsa, Cif Bisi Egbeyemi.

An fara bikin ne daa karfe 11:00am.

Hukumomin tsaron sun hada day an sanda, DSS, NSCDC da sojoji a wajen taron da ake gudanarwa a Okeyinmi, Fajuyi Park dake hanyar sakatariya.

Ku biyo mu a man hajar mu ta Facebook: https://facebook.com/HausaFinest Blog

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button