Labaran siyasa

‘Yan Social Media sun fara canja Sheka a Nijeriya

Daga Kin Gaskiya sai Bata. 
Daga. Datti Assalafiy 
Allah Ya shaida, kuma wadanda suke biye da ni a wannan kafar sun shaida, Datti Assalafiy ya jurewa zagi da cin mutunci da barazana, tun watanni uku da suka gabata nake fitar da bayanai ina ba da shawara ga mataimakan shugaba ‘kasa Buhari kan cewa su kula da masu musu hidima a duniyar social media domin muhimmancinsu a wannan tafiyar idan ba haka ba ‘yan adawa zasu janyesu, amma an kasa karban shawarar.
Abin da mu ka fahimta a gwamnatin Baba Buhari Maigaskiya shine duk wani ‘dan social media an daukeshi cima-zaune kuma zauna gari banza ‘dan jagaliyar siyasa marassa aikin yi, wanda idan aka watsa musu wani ‘dan canji kamar kaji shikenan magana ta kare, alhali wallahi sam ba haka bane.
Cikin ‘yan social media da suke yi wa gwamnatin Buhari hidima saboda soyayyar da suke masa don Allah na tabbata akwai masu aikinyi, akwai ‘yan jarida masu zaman kansu, akwai ‘yan kasuwa da manoma, kuma mutanene masu mutunci da albarka, abinda suke bukata kulawa a nuna musu an san sunayi, idan wata alfarma tazo a shigo dasu don su mora, amma idan wani abu yazo mai amfani sai ku dauki ‘ya’yanku da ‘ya’yan masu uwa a gindin murhu, ko a addinance an yarda da yin ihsani ga wanda yake maka hidima.
Babu irin rubutun da banyi ba don gwamnatin shugaba Buhari ta nunawa ‘yan social media kulawa kamar yadda take kula da ma’aikatan fadar shugaban ‘kasa, amma akayi watsi da shawarar duk da na tabbata shawaran ta kai garesu, amma anyi watsi da ita saboda watakila har yanzu gwamnatin Buhari bata gama fahimtar tasirin da social media yake dashi a wannan zamanin ba.
Akwai wasu manyan shugabannin ‘kasashen duniya wanda har mukamin minista mai kula da harkokin facebook sun nada, saboda sanin muhimmancin facebook din, akwai kasashen da anyi amfani da kafofin sada zumunta irin su faebook aka canza gwamnati, akwai kasashen da akayi amfani da social media aka kafa sabuwar gwamnati, kwanannan a ‘kasar Turkiyyah anyi amfani da ‘yan social media aka dakatar da yunkurin wasu sojoji da sukayi niyyar yin juyin mulki.
Wannan kadan kenan daga cikin tasirin da social media yakeyi a wannan zamanin, gwamnatin Buhari ta fahimci wannan, kuma a ‘dan wannan lokacin da kwanakin da basu kai 50 ba za’ayi zaben shugaban ‘kasa a Nigeria, ‘yan adawa zasu iya yin amfani da ‘yan social media ayiwa gwamnatin shugaba Buhari muguwar illa.
Jiya ‘dan gidan Atiku Abubakar yazo har Kano ya tafi da babban ‘dan social media na Buhari tare da tawagarsa, a duk karshen wata engagement dinsa a facebook yana kusan kawai miliyon ashirin, an janyeshi tare da yaransa, yanzu haka mataimakin Alhaji Atiku Abubakar Mr. Peter Obi ya iso birnin Kano domin ya tafi da wasu ‘yan social media na Baba Buhari.
Wallahi muddin gwamnatin shugaba Buhari tayi sake aka tafi da ‘yan social media na Buhari reshen jihar Kano kadai ba karamin asara mukayi ba, don aikin kanfen din da ‘yan social media reshen jihar Kano zasu yiwa shugaba Buhari yafi na wanda shugaban kanfen na Buhari wato Rotimi Amechi zaiyi.
Ku nunawa ‘yan social media kulawa, ku kirasu fadar shugaban kasa ku zauna dasu, kuce musu kun gode sannan ku musu ihsani, amma kun kasa saboda kun daukesu zauna gari banza, a daidai lokacin da a tsakanin wata guda kun kira ‘yan hausa film da mawaka har zuwa fadar shugaban ‘kasa kunyi zama dasu kusan sau uku kun kyautata musu, duk da hidimar da suke muku bai kama kafar na ‘yan social media ba.
Har yanzu gwamnatin shugaba Buhari tana da lokaci kankani da ya rage mata ta gyara wannan babban kuskure da ta tafka na yin watsi da ‘yan social media, kuma kar kowa ya kuskura yaga laifin wani ‘dan social media na Buhari da ya dena tafiyar ya koma ga ‘yan adawa tunda siyasa ce, ni Datti Assalafiy nawa bincike ne da bada shawara, idan an gyara daidai ne, idan ba’a gyara ba to masu karin magana suna cewa ”dan hakkin da ka rena watarana shi zai tsole maka ido kayi ta zubar da hawaye”
Yaa Allah Ka bamu shugabanni na gari Amin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button