Labaran wasanni

Yakamata Magoya Bayan Chelsea Su Girmama Mourinho – SarriMai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Maurizio Sarri ya ce takwaransa na Manchester United Jose Mourinho ya cancanci a mutunta shi saboda yana daya daga cikin gwanaye a duniya. 

A wani taron manema labarai da kociyan na Chelsea ya yi a ranar Asabar Sarri yace idan ana Magana akan Mourinho ana Magana ne akan mai koyarwar daya samu nasarar lashe kowanne kofi. 

Mourinho Ya yi nasara a ko’ina Saboda haka masu koyarwa suna mutunta shi kuma yanada girma kamar yadda ragowar masu koyarwa suke da ita ‘’Mourinho Kociya ne mai kyau sosai, hasali ma daya daga cikin fitattu a duniya saboda haka yana bukatar magoya bayan Chelsea su mutunta shi duba da irin abinda yayi a kungiyar.

’’ In ji Sarri A ranar Asabar ne Manchester United ta ziyarci tsohuwar kungiyar Mourinho, Chelsea a Stamford Bridge, duk da cewa kociyan dan Portugal yana cikin matsin-lamba ya sauya yadda al’amaru suke a kungiyar wadda ta yi nasara hudu kawai a wasanta takwas na firimiya amma suka buga 2-2 a wasan.

A wasan dai anyi rikici tsakanin Mourinho da wani mataimakin kociyan Chelsea bayan da mataimakin yaje gaban Mourinhi yana murna bayan Chelsea ta farke kwallonta ta biyu a daidai minti 96 da wasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button