Labaran Duniya

Yadda Na Rasa Mijin Aure Sakamakon Talle, In Ji Wata Budurwa

Mazaje Na Kaurace Wa mata masu Talle-

Khadija Adamu

*Ba Zan Iya Auren ’Yar Talle Ba – Yusuf Muhammad
*Mazan Ma Ai Su Na Son Mata Masu Sana’a – Fatima Abdullahi
A wannan rahoton musamman da wakilinmu ya hada mana, kan illolin da tallace-tallace ke janyo wa ga ‘ya’ya mata a fadin kasar nan, wata budurwa ta bayyana ma sa cewa a dalilin wannan dabi’a ta talle ne ta rasa mijin aure. Wadanda lamarin ya shafa sun kuma tafka muhawa kan hakan, inda wasu da dama suka nuna cewa alfanun da tallah ke janyo wa ga ‘ya mata illarsa ta fi amfaninsa yawa.
Bincikenmu ya gano mana cewar iyaye mata da daman gaske suna tilasta wa ‘ya’yansu yin talle ne domin samun taro-sisi, a wasu lokutan iyaye maza ke kin sauke nauyin da Allah ya daura musu na kula da iyalansu, wanda hakan ke kaiwa ga iyaye mata neman mafita ta ko halin kaka.
Sau tari, iyaye mata sukan tsunduma neman mafita ne ba tare da nazarin mene ne zai je ya dawo ba, wasu sukan daura wa yaransu talleh tun suna kasa da shekaru biyar, wanda hakan yakan kai ga lalacewar tarbiyya, jefa yara ga ‘yan garkuwa, lalata da yara, jefa wa yaran son kodi, rashin girmama na gaba, cere wa yara sha’awan karatu, da dai sauran illolin da tallah ke janyowa.
Matsalar tallah ta fi illa ga ‘ya’yan Hausawa, domin mafiya yawan lokuta Hausawa sukan so kudaden riritawa ba tare da nazarin wacce sana’ace ta dace da mace ta yi domin kare martabarta da kimarta ba; a wani binciken da wakilinmu ya yi, ya gano cewar mafi yawan matan da suke gudanar da kananun sana’o’in cikin gida irin su markade, saida abinci a cikin gida, kayan miya, waken suya, sarrafa salubai, dinki, saka da sauran sana’ar da mata ke yi a gidajen aurensu irin wadannan sana’ar kan rufa wa matan asirinsu ba tare kuma da sun jefa yaransu harkar tallace-talla ce ba.
Binciken namu ga kai ga gano cewar a karshe dai sakamakon da tallah ke fitarwa ga ‘ya’ya mata baida wani fa’ida, domin rayuwarsu yakan kasance cikin garari da kuma rashin madafa, domin wasu sukan rasa mazajen aure na gari da sauran illolin hakan.
A bisa haka ne wakilinmu ya jiyo ra’ayoyin wasu jama’a kan wannan batun da kuma yadda za a kai ga rageshi. Shin Wacce Daraja Mace Mai Tallah Ke Da Shi? Ga yadda wakilinmu ya hado mana ra’ayoyin jama’a.
Wani matashi mai suna Yusuf A. Muhammad da ke zaune a unguwar Abujan Kwata a cikin garin Bauchi ya bayyana cewar sam koda wasa baya sha’awar auren mace mai tallah, “Duk inda ka tarar da mace mai tallace-tallace za ka samu tarbiyyarta bai kai ta zauna da kowa lafiya a gidan miji ba. sau tari, mata masu tallah sukan kasance ne idonsu a bude, amma mu a da mun sani mace ba ta son daga ido ta tsura wa mijinta ko sauranta ido, yau a sakamakon tallah mace sai ta wanka maka mari ma ba wani abu ba ne.
“Don haka gaskiya ni bana sha’awar na auri mace mai tallah. Amma abun da ke damuna iyayenmu maza sune basu sauke nauyin da ke kansu na kula da iyalansu, idan na magidanci ya sauke nauyin da ke kansa uwa ma ba za ta so ta tilasta wa ‘ya’yanta tallace-tallace ba, domin ta san darajarta da kimarta na zubewa kasa,” Inji Yusuf
Yusuf Muhammad ya shaida cewar mata masu yin tallah basu da wani daraja ga samari, yana mai bayanin cewar a kowani lokaci kudin goro ake yi wa dukkanin matan da suke tallace-tallace.
Wata budurwa mai suna Khadija Adamu wacce take zaune a kauyen Miri a cikin garin Bauchi ta shaida cewar suna fuskantar barazanar rasa mazajen aure a sakamakon yaiwatar tallace-tallace, tana mai shaida cewar ana lalata rayuwar yara mata a sakamakon tallah.
Ta ce; sau tari ana yi wa mata masu tallah kudi goro da cewar suna iskanci, “Wasu iyayen mazan babu ruwansu ko ‘yarsa ta yi karatu ko karta yi babu ruwansa, wasu iyayenmu matan suna kokarin taimaka wa yaransu babu yadda za su yi kuma sai sun nemo hanyoyin da za su tafiyar da rayuwarsu. ta haka ne suke daura wa ‘ya’yansu talle.
“Su ma iyayenmu mata suna da tasu matsalar, wani lokacin idan suka daura mana talla muka je ba a samu damar sayarwa dukka ba, sai su tursasa wa yarin mene ne ya sanya ba ta sayar dukka ba, ka ga wata rana dole ne ta nemi saukin yadda za ta saida, wanda hakan ke matukar jefa mu cikin yanayin da ake mana fyade da sauran illolin ababen da ka iya bata mana rayuwa,” Inji Khadija Adamu
Budurwar ta daura da cewa, “Nan Miri masu yin aikin hanya sun yi wa yara mata masu talla fyade sosai, wanda kuma ban sani ba ko an dauki mataki a kai, ni da kaina na san an yi wa yara mata biyu fyade. Wannan lamarin na bata mana rayuwa gaya,” Kamar yadda ta bayyana
Ta kuma kara da cewa, suna fuskantar barazana ta fuskacin rasa mazajen aure a sakamakon tallace-tallace, “Yawancin samari basu son auren ‘ya’ya mata da suke tallah, domin su samarin sune ke fyade wa matan, ta yaya ne sun gama sanin halin da kike ciki kuma za su aureki a karshe. Don haka muna fuskantar matsaloli, ina kira ga yayenmu su daina tilasta mana don mu yi tallace-tallace baya haifar mana da da mai ido gaskiya,” Inji Khadija
Ita kuwa wata budurwa Fatima Abdullahi daga unguwar Abuja Kwata mai tallar saida Masa ta shaida mana cewar duk da tallah na da matsala amma wasu mazajen suna son mata masu sana’a domin za ta taimakesu wajen gudanar da rayuwar gida, “Ina tallar Masa ne domin neman rufin asirin rayuwa. Neman abun kaina da rufin asiri na ya sanya ni nake tallah. Kai tsaye ba zan ce na rasa a gidanmu ba, amma kawai ba sai na jira wani ya yi min ba,” Inji ta
Fatima Abdullahi ta ce tana kokarin kare kanta daga masu kokarin auka musu a lokacin da suke hada-hadar saida kayan tallarsu, “Ai mun san ta wuraren da muke shiga mu je mu yi sana’armu mu dawo. Ni ina zuwa tashan Mass da irin su Awala.
“Yadda na ke saida Masa ta kuwa shine, na kan fita da safe wajajen karfe bakwai na safe kafin karfe tara ko goma na dawo gida. Ina kuma sarrafa jarin mahaifiya ta ce, a duk ranar da na je tallah ban saida dukka ba bata cika min fada ba domin ta san ciniki na Allah ne,” Inji Fatiman
Ta kuma fadi irin halin wasu iyayen, “wasu iyayen idan suka daura wa yaransu talla, idan basu saida ba ko kuma kudin tallah ya fadi sai su ce ka fita ka je ka nemo musu kudinsu; idan ka fitan nan baka san yadda za ka je ka samo kudin ba; hakan na iya jefa yarinya cikin damuwa,” Inji Budurwar.
Matashi mai sana’ar tallace-tallacen, ta bayyana cewar suna fuskantar barazanar rasa mazajen aure, “Tabbas wasu mazajen basu son auren ‘ya’ya mata masu tallah, amma kuma su ma kansu mazan suna son mace mai sana’a,”
Ta ce, takan samu dan karamin lokacin zuwa makarantar Islamiyya, amma bata makarantar boko, “ina samun lokacin karatun Islamiyya. Ni yadda nake yi idan na miji ya tunkareni ya ce yana sona a wajen tallah, nakan ce masa ya rabu da ni domin nan ba wajen hira bane, ya zo gidanmu in na sona. Ni yanzu ba zai iya shaida maka nawa na tara ba, domin ina samun ribane ina kashewa,” a cewar ta
Wata budurwa da ta nemi mu sakaye sunanta, ta shaida mana yadda ta rasa mijin aure a sakamakon ta taba yin tallah, “Hum, ‘cikin damuwa’, na rasa mijin da ya gama shirya zai aure ni saura wata biyu zuwa uku a daura mana aure y ace ya fasa aure na. dalili da aka tambayeshi ya ce wai ya bincika na taba yin tallah wata shida da suka wuce kafin haduwata da shi. Wannan abun ya dameni a rayuwata amma na maida komai ba komai ba. amma ni da tallah kam har abada,” Inji ta
Hajiya Fatsuma Aminu Muhammad daya ce daga cikin kusoshi a kungiyar mata musulmai FOMWAN reshen jihar Bauchi ta shaida wa wakilinmu hanyoyin da za a bi wajen kyautata rayuwar ta fuskacin inganta inganta musu sana’arsu ba tare da sun sanya ‘ya’yansu tallace-tallace ba.
“Idan da kowace mace za ta rungumi kananan sana’o’in cikin gida hakan zai kai ga kyautata sana’ar mata ba kuma tare da yara sun je yin tallace tallace ba. amma illar da tallace-tallacen ‘ya’ya mata ke janyowa al’umma suna da tarin yawa,” in ji ta.
Kucigaba da kasancewa damu domin samun Labarai da dumi duminsu
Ku biyo mu a dandalin mu na facebook/HausaFinest Blogata budurwa da ta nemi mu sakaye sunanta, ta shaida mana yadda ta rasa mijin aure a sakamakon ta taba yin tallah, “Hum, ‘cikin damuwa’, na rasa mijin da ya gama shirya zai aure ni saura wata biyu zuwa uku a daura mana aure y ace ya fasa aure na. dalili da aka tambayeshi ya ce wai ya bincika na taba yin tallah wata shida da suka wuce kafin haduwata da shi. Wannan abun ya dameni a rayuwata amma na maida komai ba komai ba. amma ni da tallah kam har abada,” Inji ta
Hajiya Fatsuma Aminu Muhammad daya ce daga cikin kusoshi a kungiyar mata musulmai FOMWAN reshen jihar Bauchi ta shaida wa wakilinmu hanyoyin da za a bi wajen kyautata rayuwar ta fuskacin inganta inganta musu sana’arsu ba tare da sun sanya ‘ya’yansu tallace-tallace ba.
“Idan da kowace mace za ta rungumi kananan sana’o’in cikin gida hakan zai kai ga kyautata sana’ar mata ba kuma tare da yara sun je yin tallace tallace ba. amma illar da tallace-tallacen ‘ya’ya mata ke janyowa al’umma suna da tarin yawa,” in ji ta.
Kucigaba da kasancewa damu domin samun Labarai da dumi duminsu
 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button