Sharhi

YADDA GWAMNA GANDUJE YA TAYA KWANKWASO MURNAR ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWARSA- Bashir Abdullahi El-bash

YADDA GWAMNA GANDUJE YA TAYA KWANKWASO MURNAR ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWARSA- Bashir Abdullahi El-bash

Tsohon gwamnan Jihar Kano, kuma tsohon sanata, sannan kuma jagoran ƙungiyar siyasar Kwankwasiyya, Injinya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya cika shekaru (63) da haihuwa a Duniya. Kuma albarkacin wannan rana, ƴan’uwa da abokin hulɗa da mabiyansa a siyasance da sauran abokan hamayya, sun aike masa da saƙonnin taya shi murnar wannan rana.

Shi ma mai girma shugabanmu, jagoran gwamnatin Jihar Kano, mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya aikewa Kwankwason saƙon taya shi murna zagayowar wannan rana da aka haife shi. Kamar yadda ya ke cewa:

“A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Kano gaba ɗaya,  mu na taya mai girma tsohon gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwarsa inda ya cika shekaru (63) yau a Duniya”.

Bayan wannan saƙon taya murna, sai kuma gwamna Ganduje ya cigaba da yin addu’ar fatan alkhairi ga Sanata Kwankwason, kamar yadda ya ke cewa:

“Mu na yi masa fatan samun ƙarin shekaru cikin ƙoshin lafiya da nasara a rayuwa ta gaba”.

Wannan saƙon taya murna da mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya aikewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi matuƙar jan hankalin al’umma a ciki da wajen Jihar Kano inda al’umma su ke mamakin sauƙin kai da kuma haƙuri da kawaici irin na mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Sai dai kuma, ga waɗanda su ka fahimci mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje tuntuni, wannan ba abin mamaki ba ne, fiye da haka ma zai iya yi, domin a tsarin rayuwa irin ta mai girma gwamna, ko kaɗan ba ya yarda siyasa ta yanke masa zumuncin da ke tsakaninsa da wasu mutane ko al’umma, balle har ta kai shi ga yin gaba da kowa.

Kuma shi da kansa ya sha faɗar cewa ba shi da wani abokin gaba a siyasa, kuma shi gwamna ne na kowa. Ya yi rantsuwa da alqur’ani mai girma zai tabbatar da gaskiya da adalci ga duk al’ummar Jihar Kano da waɗanda su ka zaɓe shi da ma waɗanda ba su zaɓe shin ba.

Kuma sanin kowa ne a Jihar Kano an jima ba a yi gwamna mai haƙuri da sada zumunci irin mai girma gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ba, domin duk inda wani abun baƙin ciki ya faru a Jihar Kano ko a wajenta in ma mutuwa ko hasara mai girma gwamna ya kan yi hanzari da gaggawar jajantawa waɗanda iftila’in ya afkawa.

Haka sha’anin samun wata ƙaruwa ta farin ciki ko aure ko samun wani cigaban rayuwa da murnar zagayowar ranar haihuwa, gwamna Ganduje ya kan yi gaggawar tura saƙonsa na taya murna ba tare da ya yi la’akari da bambancin jam’iyya ko wata hamayya irin ta siyasa ba. A wasu lokutan har ma da kansa ya ke takawa ya je jajen ko taya murnar.

Al’umma za su iya tunawa a baya, Kwankwaso ya sha sukar gwamna Ganduje da kalmomin ɓatanci da isgilanci ga iyalan gwamna Ganduje, amma saboda haƙuri da kawaici irin na mai girma gwamna sai ya maida martani cikin raha da wasa da dariya ba tare da nuna ɓacin rai da damuwa ba.

Sannan duk irin ɓatancin da ƴan Kwankwasiyya su ke yi masa, haka ya haɗu da su a filin sauka da tashin jiragen sama na tunawa da marigayi Mallam Aminu Kano da ke Kano a kwanakin baya ya karɓe su cikin walwala da farin ciki ba tare da ya nuna musu wata damuwa ko ƙiyayya ba.

Dan haka ko kaɗan ba abin mamaki ba ne don mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya taya tsohon gwamnan Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso murnar cikarsa shekaru (63) da haihuwa a duniya ba.

Domin wannan abu ne mai sauƙi a wurin mai girma gwamna, saboda ba ya ɗaukar siyasa da gaba kamar yadda wasu ƴan siyasar su ke yi. Kuma wannan shi ne halin dattako da nagartar jagora nagari ya zamto mai sauƙin kai da haɗiye fushi gami da taya abokan hamayyar siyasarsa baƙin ciki ko murna a duk lokacin da ɗaya daga ciki ta same su. Madallah da Baba Ganduje, shugaba nagari abin koyi ga kowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button