Labaran siyasa

Yadda Aka Yi Na Rasa Damar Zama Gwamna A Shekarar 1999 – Gwamna Ganduje

Yadda Aka Yi Na Rasa Damar Zama Gwamna A Shekarar 1999 – Gwamna Ganduje.
Daga Bashir el-Bash
Yau Asabar, 6 ga watan Octoba, 2019.
A ya yin wani taro karo na bakwai (7) da aka gudanar a cibiyar dimokaraɗiyya da bincike gami da horarwa da ke (Mambayya House) kan tunawa da tsohon gwamnan Jihar Kano na farko na farar hula, marigayi Alhaji Abubakar Rimi, a ranar Talata, 5 ga watan Afrelu, 2017, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana abubuwan da su ka faru da shi game da takararsa ta gwamna a shekarar (1999) a wannan rana.
Gwamna Ganduje, ya bayyana cewa dukkan wasu alamun nasara da ƙwarin gwiwa sun bayyana zai iya zama gwamnan Jihar Kano a shekarar (1999), kuma gwamnan farko na farar hula a Jihar Kano, marigayi, Alhaji Abubakar Rimi ya na bayansa ɗari bisa ɗari, amma sai wasu daga cikin mutanen jam’iyyar (PDP) su ka nuna cewar sam ba haka ba, ba su yarda Gwamna Ganduje ya zama ba, sun nuna fusatarsu a kansa.
Sai dai kuma, daga baya waɗannan mutanen da su ka nuna ƙiyayyar tasu a kansa, sun yi da-na-sanin abin da su ka aikata, sun kuma dawo sun nemi gafararsa. Kamar yadda ya ke cewa:
“A shekarar (1999), marigayi Alhaji Abubakar Rimi ya goyi bayan na zama gwamnan Jihar Kano, amma wasu su ka ce sam ba haka ba, su ka tsane ni, na ga ƙiyayya a fili a ya yin da jam’iyyarmu ta gudanar da zaɓen fidda gwani a ƙaramar hukumar Gabasawa”.
“Sai dai daga baya sun dawo tare da neman na yafe musu kan abubuwan da su ka aika ta gare ni a baya, ni kuma na yi imani mutum zai iya zama gwamna ne a lokacin da Allah ya ƙaddara masa ya zama”. Inji Gwamna Ganduje.
Bayan abubuwan da su ka faru a wannan lokaci, gwamna Ganduje shi ne ya yi wa tsohon gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso mataimakin gwamna na zangunan mulki biyu daga (1999-2003) da kuma bayan dawowar Kwankwason kan madafun iko.
Gwamna Ganduje, ya kuma ƙara da cewa a wancan lokaci, ya na da matuƙar kusaci da marigayi Alhaji Abubakar Rimi saboda hulɗar zamantakewa da nazarin al’amura. Sannan kuma ya cigaba da cewa: “Tarihi ba zai taba mantawa da magabacin ɗan siyasa mai nagarta da kykkyawar manufa, mutum mai ƙaunar mutanen da ba kowa ba a cikin ruhinsa ba.
Daga nan kuma, gwamna Ganduje ya ƙara da cewa, marigayi Alhaji Abubakar Rimi ya bar abubuwan cigaba da dama a tsohuwar Jihar Kano, gwamnatinsa ta yi ayyuka da samar da tsare-tsare masu muhimmanci, kamar samar da shirin ilimin manya, da samar da kamfanin samar da kayayyakin noma na Jiha da kuma ɗumbin manyan ayyukan raya Jiha.
Mai martaba Sarkin Kano, wanda ya samu wakilcin tsohon gwamnan Jihar Kano, kana kuma Sanata a halin yanzu, Mallam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, ya bayyana marigayi, Alhaji Abubakar Rimi a matsayin shugaba nagari, wanda hatta ƴan hamayya ma sun gamsu da gaskiyarsa.
“Marigayi Alhaji Abubakar Rimi, jagoranmu ne, wanda ya ke sauraron shawarwari daga na ƙasa da shi, a kwai buƙatar mu kasance masu koyi da shi a ya yin da mu ke cikin gwamnati”. Inji Sardaunan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, wanda ya wakilci mai martaba sarkin Kano a wancan lokaci.
Wannan kaɗai, ya isa ya sanya matasan Kwankwasiyya waɗanda ba su san tarihi ba su gane cewar tun asali Gwamna Ganduje ba yaron Kwankwaso ba ne, hasali ma, Gwamna Gandujen shi ne mai gidan Kwankwaso. Kuma ba Kwankwaso ne ya yi wa Gwamna Ganduje alfarma ya ba shi mataimakin gwamna ba, lala, Gwamna Ganduje ne ya yi wa Kwankwaso alfarma ya karɓi mataimakin Gwamna.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button