Labaran Duniya

Ya rage na ku: Sheikh Gumi ya ba Musulmai shawaran wanda za su zaba a 2019

Mun samu labari cewa babban Malamin nan na addinin Musulunci Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi yayi magana kan wasu batutuwa a Najeriya wanda su ka hada da babban zaben da za ayi a 2019.

Babban Shehin yayi wannan jawabi ne lokacin da yayi karin haske na zuwan sa wajen wani sulhu da aka yi tsakanin Atiku da Obasanjo a Jihar Ogun. Malamin dai ya nuna cewa Musulunci yayi na’am da abin da yayi dari-bisa-dari.
Ahmad Abubakar Gumi ya nemi Jama’a su duba halin da su ke ciki, su zabi irin Shugaban da su ka ga ya dace da su. Gumi yace idan har mutum ya ga yana cikin jin dadi da walwala, sai ya zabi wannan Gwamnati ta cigaba da mulki.
Hakan nan kuma Malamin yace idan har mutum yana cikin wani mawuyacin hali, sai ya nemi ya rabu da wannan Gwamnati ya zabi wata. Malamin yace ba zai tursasawa kowa, ko ya fada masa wanda zai zaba a mulki a zaben 2019 ba.

Shehin dai yace yana gudun yi haka ne ka da gobe a dawo a ce shi ya jefa jama’a cikin halin da aka shiga don haka yace kowa ya zabi wanda yake ganin kakar sa za ta yanke masa saka ya na mai cewa kowane yayi amfani da damar sa da kyau.
Kwanan nan ne aka hangi Atiku Abubakar da wasu ‘Yan PDP tare da Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi da kuma Bishof Mathew Hassan Kukah a cikin jirgi zuwa wajen Cif Olusegun Obasanjo.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button