Raayi

Ya kamata a zaftare yawan ‘yan majalisun tarayya idan ana son Najeriya ta bunkasa ~ Rochas Okorocha

Ya kamata a zaftare yawan ‘yan majalisun tarayya idan ana son Najeriya ta bunkasa ~ Rochas Okorocha

Tsohon gwamnan jihar Imo kuma sanata mai wakiltar jihar Rochas Okorocha ya nemi da a rage zauren majalisar tarayya zuwa daya idan an son ci gaban Najeriya da gaggawa. Inda ya cewa kasar nan ba za ta jure daukar dawainiyar majalisun biyu ba.

Hausa Daily Times ta ruwaito cewa Sanata Okorocha ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke bada gudummawa game da rahoton da kwamitin MTEF na majalisar dattawa ya kawo a jiha Alhamis a zauren majalisar. Ya nemi da a rushe majalisa bangaren na wakilai domin a cewarsa dan majalisar wakilai da Sanata na gudanar da abu iri daya ne.

Da yake mai da martani kan rashin aiwatar da wasu kasafin kudi na 2019 da kwamitin majalisar kan kasafin kasa da tsare tsare ya gabatar bisa rashin isassun kudade, Sanatan ya ce gwamnati na kashe makudan kudade kan ‘yan majalisu.

A cewarsa ” Mai girma shugaban majalisa, ‘yan uwana Sanotaci, ya kamata mu fada wa kanmu gaskiya. Mu dubi adadin ‘yan majalisun dattawa da na wakilai? “
A gareni, wani abu ne mai matukar muhimmanci da dan majalisan wakilai ke yi da Sanata ba ya yi?

Sanata Rochas Okorocha ya bayyana cewa yanzu lokaci ne da ya kamata su nuna sadaukar wa kasar su.  Inda ya kara da cewa Sanata daya ya isa ya wakilci jiha domin rage barnatar da kudi da gwamnatin tarayya ke yi a kansu.

Ya ci gaba da cewa, kamata ya yi gwamnati ta rika kashe irin wadannan makudan kudi a bangaren da za ta samu karin kudaden shiga ga kasa ba a inda za ta rika barnatarwa ba.

Da ya ke mayar da martani ga korafin Rochas Okorocha, Shugaban majalisar ta dattawa Dr. Ahmad Ibrahim Lawan ya bayyana cewa doka kasa ce ta samar da wadannan majalisun,  inda ya ce ww Sanata Rochas Okorocha cewa ya na da ‘yancin gabatar da kudirin neman zaftare majalisar a mai da ita gida daya kamar yadda Hausa Daily Times ta ruwaito.

Shugaban ya kara da bayyana cewa, an samar da majalisun biyu ne domin baiwa kowani dan majalisa damar zaurafafa tunaninsa domin amfanar da kasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button