Labaran wasanni

Wenger Zai Koma Kungiyar Wasa Ta AC Milan

Tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger, yana shirin maye gurbin Gannaro Gattuso a matsayin kociyan kungiyar kwallon kafa ta AC Millan kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Mista Wenger dai ya kasance baya koyar da kowacce kungiya kawo yanzu tun bayan daya kawo karshen zamansa na shekara 22 a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a karshen kakar data gabata.

AC Millan dai karkashin mai koyarwa Gattuso bata fara buga kakar wannan shekarar da kafar dama ba bayan data samu nasarar wasa daya acikin wasanni biyar na farkon kakar nan sai dai daga baya kuma ta samu nasara a wasanni biyar cikin wasanni shida da kungiyar ta buga a baya.
Kawo yanzu dai kungiyar kwallon kafa ta AC Millan tana matsayi na hudu a gasar ta siriya A kuma za ta kai ziyara kungiyar kwallon kafa ta Jubentus wadda take mataki na daya a gasar a wannan satin.
A kwanakin baya dai kungiyar AC Millan ta bayyana Iban Gazidiz a matsayin sabon daraktan kungiyar wanda kuma tsohon daraktan Arsenal ne wanda yaso a kori Wenger a Arsenal lokacin yana kungiyar.

Sai dai idan har Wenger ya koma kungiyar zaiyi aiki ne tare da tsohon dan wasan kungiyar Leonardo wanda yayi aiki da kungiyar kwallon kafa ta PSG ta kasar Faransa shekarun baya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button