Labaran wasanni

Waye Zai Fara Barin United Tsakanin Pogba Da Mourinho?Rikici yau rikici gobe tsakanin dan wasa Poul Pogba da kochin Manchester United Jose Mourinho ya haifar da rashin jituwa tsakaninsu tare da haifar da rashin jin dadi ga magoya bayan kungiyar dake fadin duniya.

Tun farkon dai daman Mourinho yana da dabi’ar kuranta ‘yan wasa idan komai yana tafiya daidai amma da zarar an samu mishkila sai ya fara kushe dan wasa gami da fadar bakaken maganganu a kansa. 

Sannan kochin yana da tarihin hada ‘yan wasa fada a tsakaninsu tare da kawo rashin jituwa a dakin shiryawar ‘yan wasa a kowacce kungiya wato (Dressing Room). 

Yayin da a gefe guda kuma shi Pogba yake takamar iya kwallo tare da buga yadda yake so a cikin fili. 

Sannan kuma yana son ya buga lambar da da zai iya shiga ko ina ba ya tsaya a waje guda ba. 
Amma kuma a gefe guda magoya bayan kungiyar da yawa suna ganin cewa matsalar daga kocin take ba daga Pogba ba, wanda hakan ta sanya suke son a kori Mourinho yabar kungiyar ko abubuwa zasu canja. 

Su kuma mahukuntan kungiyar na tunanin makudan miliyoyin kudin da korar tasa zai zukarwa lalitarsu sannan kuma Pogba ya ce indai Mourinho ya ci gaba da zama a kungiyar zai bar Ingila hakan yasa yanzu dai tuni manyan kungiyoyi suka shiga zawarcin sa cika har da tsohuwar kungiyarsa ta Jubentus da kuma Barcelona. 

Daga nan zuwa farkon sabuwar shekara ne dai ake sa ran komai zai iya faruwa, ko dai a sayar da Pogba ko a kori Mourinho ko kuma su duka biyun su bar kungiyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button