Labarai

WATA SABUWA: Asirin Wadanda Suka Dauki Nauyin Kirkirar Bidiyon Karya Ga Gwamna Ganduje Ya Soma Tonuwa

Daga M Inuwa MH

Rahotanni Sun Nuna Cewa Wasu Manya Guda Uku Ne Suka Dauki Nauyin kirkirar Bidiyon Karya Ga Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Bincike Ya Nuna Cewa Bidiyon Ya kai Kusan Kwana Goma Ana Aikin Kirkoro shi. Inda Aka yi Amfani Da hikimar Zamani.

Na san Mai Karatu Zai Fahimta Tare Da Imani Cewa A Zamanin Da Muke Ciki Na Yanzu Akwai Na’urorin Zamani Da Suke Shigowa Kala Kala Wanda Ake Sarrafa su Da Na’ura Mai Kwakwalwa (Computer) Domin Canja Halittar hoto Mai Motsi Ko Mara Motsi. Wannan Fasaha Ta kai Matukar Kwarewa Wajen Canja Halitta har ta kai Ga Cewa Ba Karamin Mai tunani Bane Zai Iya Ganewa A Lokacin Da aka yi kwaskwarima Ga Hoto Mai Motsi Ko Mara Motsi.

A Kowacce Shekara Ko Kuma Na ce A Duk Lokacin Da Wani Sabon Abun Al’ajabi Ya Shigo Nijeriya ko Makamancin Haka, Wannan Abu Yana Zama Wani Abin Mamaki da Rikitarwa Ga Al’ummarmu Domin Kasancewar mu Masu Karancin kayan Cigaba A wannan kasa Tamu Mai Albarka.

Haka Zalikama Wannan Abu Yana Zama Abun Cece Kuce da Kuma Abun KaryataJuna Ta Hanyar Musanta juna. Domin Wasu Za su ce Irin Haka Ba zai Taba yuwuwa Ba. Amma Idan Al’amarin Ya Zama Gama Gari Sai ka ji Kowa Ya Yarda Da Hakan.

Maganar Gaskiya Bidiyon Da Aka Nuna Gwamna Ganduje Yana Karbar Dala Na Karya ne. Kuma Idan Baku Manta Ba A Baya Na yi Muku Bayani Game Da Bidiyon da Duk Yadda Aka yi Wasa Da Hankalin Al’umma tun Kafin A Saki Wannan Bidiyo. Kuma Kun ga Abinda Na Fada Ya Faru A ciki Kamar Yadda Na Bayyana Maku A Baya.

Bincikemu Ya Nuna Mana Cewa Manya Mutun Uku Ne Suka Dauki Nauyin Wannan Bidiyon Daga Cikinsu  Mutum Biyu Yan Jihar Kano ne Mutun Daya Dan Jihar Zamfara Ne. Mutum Na Farko Ya Daura Damarar Yaki Da Gwamna Ganduje Ne Samakon Faduwa Zaben Cikin Gida Da ya yi na Jam’iyar Ta APC Wanda Yake Zargin Cewa Gwamna Gandujen Ne Silar Faduwar Tashi.

hidai Wannan Mutun Daya Fadi Zaben Cikin Gidan Na Jam’iyar APC Shi Ya Kasance  Dan Cikin Gidane A Gidan Shugaba Mohammadu Buhari…

Mutum Na Biyu Shima Yanzu Haka Yana Rike Da Wata Ma’aikata A Cikin Wannan Gwamnatin Ta Shugaba Buhari Kuma Dan Gatan Buhari Ne Haka Zalika Dan Jihar Kano Ne. Labarin da ya zo Mana Shine Cewa Wannan Mutum Shima Yana so A Gogawa Gwamna Ganduje Kashin Kaji Ne Domin tsakanin Gandujen Da Buhari Su Samu matsala. Inda Shi Kuma Zai yi Amfani Da wannan Damar domin Jam’iyyar APC Ta Kwace Tikitin Takara Daga Hannun Gwamna Ganduje Ta Ba shi Takara A Zaben 2019. Wannan Mutum Ya Fito ne Daga Shiyyar Kano Ta Arewa.

Mutun Na Uku Kuma Yanzu Haka Yana Da Mukamin A Ofishin Uwar Jam’iyya Na Kasa, Wanda Shine Yanzu Haka Ya yi wa Wancan Mutumin Da ya Fito Daga Kano Ta Arewa Alkawarin Ba shi Tikitin Takara Bayan An Kwace Tikitin Gwamna Ganduje Na Tsayawa Jam’iyar APC Takara.

Nan Gaba Za mu Bayyana Sunayen su Tare Da Hujja Domin Komai Akwai Ka’ida.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button