Labaran Duniya

Wata kyakkyawar budurwa ta bata ana daf da daura mata aure a Kaduna

Wata tsaliliyar budurwa mai kananan shekaru da kuma ake daf da daura mata aure a unguwar Barnawa, garin Kaduna mun samu labarin cewa ta bace tun ranar Lahadin da ta gabata.

Kamar dai yadda muka samu, budurwar wadda ke zaman ‘ya ga Sarkin unguwar ta Barnawa a bangaren gidaje masu saukin kudi wata Low Cost, an ce ta bace ce lokacin da ta ce za ta je karbo dinki a sha-tare-talen Amingo duk dai a garin na Kaduna.

Rahotannin Hausa dai ya samu cewa garin na Kaduna na cikin garuruwan da satar mutane da garkuwa da su ya yawaita a yan shekarun nan duk kuwa da kokarin da gwamnatocin tarayya da na jihar ke ikirarin yi game da batun.

Haka ma ranar Juma’a ne muka smau wani labarin cewa wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko suwa ye ba sun sace babban basaraken nan na al’ummar Adara, watau Agwon Adara mai suna Mai Martaba Maiwada Galadima III ranar Juma’a.

Mun samu cewa dai an sace basaraken ne tare da matar sa yayin da suke kan hanyar su ta zuwa Kachia daga garin Kaduna, babban birnin jihar cikin motar su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button