Kannywood

WASHA, ALI NUHU DA RAHAMA SADAU SUN LASHE KYAUTAR GWARAZAN SHEKARA A INGILA

WASHA, ALI NUHU DA RAHAMA SADAU SUN LASHE KYAUTAR GWARAZAN SHEKARA A INGILA
Fitattun jaruman fina finan Hausa, Fatima Abdullahi da aka fi sani da Fati Washa da Ali Nuhu wadanda su ka lashe kyautar gwarazan jaruman finafinan Hausa na shekarar 2019 da kuma Raham Sadau wacce ta Karbi kyautar fitacciyar Jaruma na wannan shekarar a wani gagarimin bikin finafinan Afirka da aka gudanar a Birtaniya.
Washa ta samu nasarar lashe kyautar ne a matsayin gwarzuwar jaruma daga fim din Sadauki wanda kamfanin Giggs Entertainments ya shirya. Karramawar ta hada da Jaruma Rahama Sadau da kuma Ali Nuhu, wanda Jamilu Yakasai ya wakilta.
Bikin wanda ake kira da Afro Hollywood Awards ya shafi karrama jaruman finafinan harsunan Najeriya guda uku Hausa da Yoruba da Igbo da kuma na Inglishi a sassan kasashen Afirka.
 Fati Washa ta lashe kyautar ne saboda rawar da ta taka a Fim din ‘Sadauki, inda ta doke Aisha Aliyu Tsamiya a Fim din da ta fito “Jamila” da kuma Halima Yusuf Atete da ta fito a “Uwar Gulma”
A tawagar tafiyar da suka yi zuwa Birtaniya dai ta hada da Rahama Sadau, Hadiza Gabon da Kuma Jamilu Yakasai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button