Labaran Duniya

Wani wanda ake zargi ya sace jaka cike da daloli a dakin Robert Mugabe

An gurfanar da mutum uku a gaban kotun kasar Zimbabwe in da ake zarginsu da satar jakar tsohon shugaban kasar, Robert Mugabe, wadda ke dauke da $150,000 (kimanin Naira Miliyan 54).
Wadanda ake zargin, sun kashe kudaden ne a kan sayen motoci, gidaje da kuma dabbobi.
‘Yar uwar tsohon shugaban, Constantia Mugabe, na daga cikin wadanda ake zargin.
Ana zargin tana da makullan gidansa da ke a kauyen Zvimba a kusa da babban birnin kasar, Harare, in da ta bai wa sauran mutanen makullan.
Sauran wadanda ake zargin masu hidimomin gida ne a lokacin da aka yi satar wadda ta auku tsakanin 1 ga watan Disamba na 2018 zuwa Janairu.
Robert Mugabe ya jagoranci kasar na tsawon shekara 37, in da wasu ke zarginsa da kwashe kudaden kasar domin jin dadin kansa.
A shekarar 2017 ne sojojin kasar suka hambare Robert Mugabe mai shekara 94.
BBC Hausa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button