Labarai

Wani annabin karya ya bayyana a Najeriya

Wasu kasurguman katta su biyu da daya daga cikin su ke ikirarin cewa shi Annabi ne masu suna Ayo Jimoh da Abdullahi Jubrila sun shiga hannun jami’an ‘yan sandan Najeriya bayan sun damfari wata mata mai suna comfort Macaulay har Naira miliyan daya.

Daga cikin kasurguman kattin dai, Ayo Jimoh shine yake da’awar shi Annabi ne wanda hakan ya sa ta yadda da shi har ta bashi kudin ta makudai domin yayi mata addu’a.

Jaridar mu ta samu cewa Jimoh din wanda ke da shekaru 45 a duniya, ya karbi Naira 266,000 a tashin farko sai kuma ya anshi sarkokin zinaren matar da suka kai Naira 750,000.

Da ya shiga hannun ‘yan sanda, Mista Jimoh ya gasgata laifin da ake tuhumar sa da shi inda kuma ya bayyana cewa shi zinaren da ta bashi tuni ya saida su kuma suma kudaden ya kashe shu.

Yanzu haka dai suna a gaban kotun majistare ta garin Ikorodu, jihar Legas inda ‘yan sandan suka gurfanar da su.

Source: hausa.legit.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button