Labaran Duniya

Wanda ya taimaki Bill Gates ya rasu

Mutumin da ya taimkawa attajirin duniya Bill Gates samar da kamfanin Microsoft ya rasu yana da shekara 65, bayan kamuwa da cutar Kansa.
Attajiri Paul Allen shi ne tushen kamfanin Microsoft wanda tare da Bill Gates suka kaddamar da shi wajajen 1970.
Mutanen biyu abokai ne tun kuriciya inda tun a makaranta a tare suka fara gina tunaninsu kan kwamfuta.

Allen ne kuma ya ja ra’ayin abokinsa Bill Gates ya fice daga Jami’ar Havard domin mayar da hankali ga aikin kamfaninsu na Microsoft
Bill Gates ya ce ci gaban kwamfuta ba zai taba yiyuwa ba, ba tare da Paul Allen ba kuma za a ci gaba da cin moriyar gudunmuwarsa ga ci gaban fasaha.
A 1983 ne ya bar kamfanin Microsoft bayan sabani da Bill Gates sai dai kuma jarinsa a kamfanin ya taimaka masa wajen bunkasa kasuwancinsa a fannoni da dama da suka hada da binciken kwanfuta da saye da sayar da gidaje da harakar wasanni da kuma kade kade.

An yi hasashen cewa mista Allen yana da dukiyar da ta kai sama da dala biliyan 20.
Bill Hilf babban jami’in wani kamfanin Mista Allen da ake kira Vulcan wanda ya kafa a 1986 ya ce shi ne ya gina masa tunani a rayuwarsa.
Ya ce bai taba haduwa da wani ba a rayuwarsa kamarsa wanda ke burin samar da abubuwa da dama a duniya, domin ya sauya rayuwrsa kuma zai ci gaba da sauyawa.
Mista Allen dai yana cikin attajiran duniya da suka bada babbar gudunmuwa ga yaki da cutar Ebola a Afrika da kuma sauyin yanayi kuma ana ganin zai ci gaba da tasiri a duniya a shekaru da dama.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button