Labaran siyasa

Tushewar Basira Ne A Ce Wai Shugaba Buhari Kwafi Ne –Gwamnatin TarayyaFadar shugaban kasa ta mayar da raddi ga masu ikirarin cewa shugaban kasa Buhari ba asalin Buhari bane, kwafi ne, wannan wauta ce kawai, kuma bai ma kamata mutane su damu da irin wadannan maganganun banzan ba marasa tushe balle makama.

Ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammad ne ya fadi hakan a yayin da yake zantawa da manema labarai yau Alhamis a garin Abuja, bayan da manema labaran suka neme jin ta bakin shi a kan wannan lamarin, inda wani dan jarida ya tambaye shi mai zai ce game da batun da ake ta yadawa cewa Buharin da ake gani ba na asali bane, wani ne na bogi mai suna Jibrin daga kasar Sudan ko cadi.
Wannan jita-jitar ta biyo bayan wata mummunar rashin lafiya da Buharin ya yi shekarar da ta gabata, amma kuma bayan wani lokaci sai ya samu sauki gaba daya, Lai Muhammad ya ce: Lallai duk gwamnatin da ta san abinda take yi ba za ta saurari wannan shirmen ba, saboda tsabar wauta ce kawai, in ba wauta ba, shi wancan Jibrin din na Sudan ko Cadi da aka ce an yi kwafin shi, yanzu ana nufin yana can Sudan din ko Cadi kenan? Wannan ba wauta bace dan Allah?
“Suna cewa wai Jibrin din daga kasar Cadi yake, yanzu haka da muke magana shugaban kasa yana Cadi, sun ce Jibrin ne, amma kuma yana iya tuna komai da ya taba yi baya, misali yana iya tuna abinda yayi lokacin yana ministan man fetur, yana iya tuna abinda ya yi lokacin da yayi shugabancin kasa a tsakaninshekarun 1983 zuwa 1985, duk yana iya tuna abubuwan da suka wakana a shekarar 1985, amma sun ce wai kwafi ne shi.’ Inji Alhaji Lai
Lai Muhammad ya kara da cewa: Jibrin dan kasar Sudan ne ko Cadi duk zai iya tuna wadannan abubuwan? Wannan zancen banza ne kawai, kuma gwamnati ba ta da lokacin ba da amsar wannan shirirtar, sannan su kansu al’umma yakamata su yi watsi da irin wannan shirme da shiriritar 


Source: leadershipyau.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button