Labaran wasanni

Tunda Ronaldo Ya Tafi Real Madrid Ta Lalace – In Ji Figo

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta Portugal, Luis Figo, ya bayyana cewa tunda kungiyar Real Madrid ta siyar da dan wasa Cristiano Ronaldo kungiyar ta lalace amma kuma yace daman hakan yana faruwa ga kungiyoyi.
Sai dai Figo ya bayyana cewa kungiyar zata iya gyara kuskuren da tayi idan har zata iya zuwa ta siyo dan wasan Chelsea Edin Hazard wanda ya nuna a fili cewa yanason komawa Real Madrid bayan kammala kofin duniya.
Real Madrid dai ta siyar da Ronaldo ne ga kungiyar kwallon kafa ta Jubentus akan kudi fam miliyan 105 bayan ya shafe shekaru tara a kungiyar kuma ya zura kwallaye 450 tare da kofuna da dama.
‘Siyar da Ronaldo yasa kungiyar ta shiga yanayin canji amma kuma daman dole sai an fuskanci irin wannan yanayi sai dai kungiyar tana bukatar siyan babban dan kwallo domin idan kayi rashin Ronaldo kana bukatar siyan babban dan wasa” in ji Figo
Yaci gaba da cewa “Ronaldo shi kadai idan yana fili yana iya sawa kungiya tasamu nasara koda ace shi bai zura kwallo a raga amma kuma zamansa a fili hatsari ne kuma yana zura kwallo a raga a lokutan da ake bukata”
A karshe yace Real Madrid ta shafe shekara da shekaru tana samun nasarar lashe kofuna saboda haka idan sun samu kansu a irin wannan yanayi ba wani abu bane haka daman wasan kwallo yake.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button