LabaraiLabaran Duniya

Tsohon Shugaban Najeriya Shehu Shagari Ya Rasu

Rasuwar shagari
Allah ya yi wa tsohon shugaban Najeriya, Alhaji Shehu Aliyu Shagari rasuwa.
Tsohon shugaban na Najeriya ya rasu ne yana mai shekaru 93 a babban asibitin birnin tarayya na Abuja.
Jikan marigayin, Bello Shagari ya tabbatar da rasuwar kakan nasa a shafinsa na Twitter.
“Ina mai alhinin sanar da ku rasuwar mai girma tsohon shugaban Najeriya, Alhaji Shehu Shagari, wanda ya rasu yanzun nan a babban asibitin Abuja.” In ji Bello.
Marigayi Shagari, shi ne shugaban Najeriya na farko na mulkin farar hula a lokacin Jamhuriyya ta biyu, wanda ya mulki Najeriyar daga shekarar 1979 zuwa 1983.
Muna tafe da karin bayani.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button