Tarihi

Tarihin Sabon Mawakin Salon Zamani – ALHASSAN M. YARIMA

TAKAITACCEN TARISHIN MAWAKI ALHASSAN M YAREEMA MAI WAKA 

Dafarko sunana Alhassan Muzammil Alhassan Wanda akafi sani da  ALHASSAN M YAREEMA MAI WAKA

Takaitaccen tarishina shine:-

  An haifeni a wani kauye mai suna KARITSALLE a garin taura dake jahar JIGAWA nayi karatun makarantar firame dina a garin taura, bayan nagama firamare Dina na Dora da karatun a makarantar sakandare Wanda cikin hukuncin Allah na kammala karatuna na sakandire a shekarar 2015
       Bayan nan na cigaba da karatun makarantar gaba sakandire Amman kafin na ci gaba da karatuna na tsinci kaina a wannan Sana’a ta WAKA

     Dalilin da yaja hankalina nashiga wannan sana’a shine:- bisa nazari da dogon tunani danai Nagano cewar WAKA Itace hanya mafi saurin isar da kowanne irin sako cikin sauki kuma cikin karamin lokaci ze kewaye nashiya zeje kunnuwan al’umma daban-daban,,,,kafin nafara WAKA nafara ne da kirkira dakuma rubuta zafafan kalamai irin na soyayya domin nishandantar da jama’a dakuma zummar kawo gyara a harkar tafiya irin ta wahainiyar da soyayya take musamman awannan zamani da muke ciki.

  Tun asalina SOYAYYA tana burgeni  kuma inason ganin masoya sun kasance tamkar hanta da jini hakan yasanya kullum nake fafutukar ganin mun wayar da kan masoya.

   Irin littafai da kuma rubutukan danake yadawa a social media akan love yasanya abokaina yan uwa da dukkan masoyana suke bani shawara akan nashiga harkar WAKA domin sakon zaifi saurin xuwa ga al’umma. Dafarko naji tsoro kafin nafara sakamakon bantabayin WAKA ba alokacin gani inke kamar baxan iyaba.

   Cikin hukuncin Allah na amsa shwarar MASOYANA Nafara wannan Sana’a alhamdulillahi xuwa yanzu nasamu nasarori masu yawa silar wannan Sana’ar ta WAKA

 wasu na tambayata aina nasamo asalin suna YAREEMA

   Asalin wannan suna  {YAREEMA} nasamo wannan suna ne tun alokacin da nake rubuta littafan soyayya A lokacin ne naji mutane suna kirana da YAREEMAN MASOYA  wannan shine asalin sunan yareema tunda daga lokacin sunan yake bina harxuwa sadda nafara waka kuma har xuwa yau masoya sune suka radamin wannan suna.

KALUBALEN DANA FUSKANTA:-
       Na fuskanci kalubale da yawa acikin Sana’ar waka  Wanda wannan narikeshi araina amatsayin kaddara ce cikin arayuwata hakan yanunamin cewar hakuri da juriya suke kai ga bawa cin nasara arayuwa.

   Hmmmm wasu suna tambaya wae shin Alhassan M Yareema inada AURE KO BABU??
      A zahirin gaskiya ahalin yanxun bani da aure kuma ina sa ran xanyi idan lokaci yayi nima nabar kwanan shago.

WAKOKINA:-
   Eh to akalla nayi wakoki xasu kai 50 wadanda na rerasu nikadai banda wadanda mukai na hadaka da yan uwa abokan Sana’a ta. Kowanne MAWAKI xaka samu cikin wakokinsa akwae wadda tafi burgesa toni anawa bangaren babu wata waka dazance tafi burgeni se wadda MASOYANA Suna dauka amatsayin wadda tafi burgesu,
   Cikin wakokina akwai wadanda mutane suke yawan yimin magana akansu hakan ya nuna min cewar sune wadanda suke burgeni abangaren Yareema wakar {MURADIN RAINA}   wadda kuma tafi karbuwa wajen al’umma itace <DIYAR ADAMAWA> Dan haka itace amatsayin BAKANDAMIYATA domin masoyana da baxarku nake taka rawa

SHAWARA GA “YAN UWANAH MAWAKA
   Shawarata garemu shine mu cire hassada,bakin ciki,da ganin kyashi mu temakawa duk Wanda mukaga yana da bukatar temako musamman acikin Sana’ar mu mukau da bangaranci se muci gaba arayu.Kar ka wulaqanta kowa domin bakasan mexe xama a gaba ba wannan kuskurene Babba mu tsaftacce harshemu base munci xarafi ko munzagi wani ba sannan muyi tunanin se tahaka xamu samu abinci.

ABINCIN DA YAFI BURGENI
    Ehemm idan aka zo bangaren girki shinkafa da wake shine abincin dayafi burgeni alabashi yadauki reko da onga banayin wasa idan nasameta.

SAKONA NA KARSHE ZUWA GA MASOYANA SHINE:-
 Zanyi amfani da wannan Dama in sanar damu sabon albums dina Dana shirya domin nishandantarku da nuna muku tsintsar qaunar danake muku hakan tasa nai masa laqabi da suna GARIN MASOYI  dashi da album din dakuka dade kuna tsimaye  wato RIGAR FULANI  sunan fitowa kujirayi xuwansu Masoyana kune abin alfahariin ALHASSAN M YAREEMA

WADANNE IRIN WAKOKI ALHASSAN YAFI RERAWA
 
Ahm ina rera wakoki maban banta kama daga kan na SOYAYYA  AURE  BIKI KO SUNA.

YADDA ZA’A GANA DA NI KAITSAYE
       Ga dukkan masu son magana ko sada xumunci dani kaitsaye ya nemi awannan lamba 08146991365  kokuma Instagram rearealalhassan m Yareema. nagode Masoyana

Ga masu WhatsApp 08146991365
    KOFARMU ABUDE TAKE SHAWARA KO WANDA YAKE BUKATAR WAKA
 

NAKHU HARKULLUM
  ALHASSAN M YAREEMA MAI WAKA

 allah yabarni daku masoyana

Salisu M. Yarima

Salisu M. Yarima

Salisu M. Yarima

Salisu M. Yarima

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button