Tarihi

Tarihin Khalifa Sheikh Isyaka Rabi’u (Khadimul Qur’an)

An haifi Sheik Isyaka Rabiu cikin shekarar 1928, a wani kauye mai suna Tinki, wanda yake cikin karamar hukumar Bichi – Duk da yake tarihin kakaninnsa sun yo gudun hijira ne daga Borno, cikin shekarar 1892, domin su guje wa kisan gillar da Rabeh yake wa mutane.
Mahaifinsa mai suna Malam Rabi’u Dan Tinki, kauyen Tinki aka haife shi. Kuma zuri’arsu sun yi fice ne wurin harkar ilimin addini.
Malam Rabi’u Dan Tinki, ya yi karatun addini ne a wurin mahaifinsa, Malam Yunusa. Amma daga baya ya tafi wani gari mai suna Inshanwa, wanda yake can Damagaram Jamhoriyar Nijar. Inda ya yi karatu a karkashin wani fataccen Malami mai suna Gwani Kalla, inda ya kwashe shekaru sha uku.
Domin Kallon Bidiyo Jana’izar Sa Ku Shiga Nan
Bayan ya gama karatunsa a can ne ya dawo gida da niyar yin aure. Bayan ya yi auren kuma ya dauki matar ya nufi wani gari mai suna Inkiluwa, wanda yake kusa da Gashua, daga baya ya nufi Katagum, sannan ya dawo Kano.
Daga Kano ya sake tattara komatsansa, ya nufi Zaria gidan wani shahararran Malami, mai suna Malam Na’iya, inda ya samu shekaru biyu yana dalibta.
Kafin Malam Rabi’u Dan Tinki ya rasu a shekarar 1959, ya rubuta littattafai kusan 50. Shi ma Malam Rabi’u Dan Tinki a lokacin rayuwarsa, ya tura Isyaku Rabi’u garin Nguru neman ilmin addinin Musulunci. Bayan kammala karatun sa ne ya dawo gida Kano, cikin shekarar 1947. Sannan shi ma yayi auren fari, sannan ya fada harkar kasuwanci da izinin mahaifinsa, kuma yana hadawa da karatu.
Abubuwa sun fara bunkasa a cikin shekarar 1958, domin ya gina gida nashi na kansa a unguwar Jakara. Abubuwa suka ci gaba da bunkasa inda ya fara zama hamshakin dan kasuwa ya rika harkar litttattafai na addini, kayan masaku, da kekunan dinki. Malam Isyaka Rabi’u Shahararren dan Tijjaniya ne, yana daya daga cikin manyan almajiran shiek Ibrahim Nyas Kaulaha, yana da jerin masa’antu, cikinsu akwai masakar Bagauda. Yana da wasu jerin gidaje na kawa, masu daukar hankalin baki, ko matafiya a kan titin Malam Aminu Kano.
Marigayi Malam Isyaka Rabi’u kafin rasuwar sa a Yammacin wannan rana ta Talata 8/05/2018 a baya, Ya dan taba harkokin siyasa a Jamhuriya ta daya. Ya yi jam’iyar NEPU, amma daga baya ya koma NPC. A Jamhuriya ta biyu ya samu kansa a jam’iyar NPN.
Haka kuma marigayin ya samun shaidar karramawa daga wurare da fannoni daban daban duba da irin gudunmawar da ya bayar wajen cigaban addinin Islama a ciki da wajen Nigeria.
Ya rasu ya bar mata hudu da ‘ya ‘ya 42.
Allah ya jikansa ya rahamshe shi.
*Littafin da ya taimaka mana wurin bincike, Kano 100 Political And Business, na Ransom Enmenari da Ibrahim Barde.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button