Labarai

Tabbas bidiyon Ganduje yana karbar kudi gaskiya ne – Jaafar

Mawallafin jaridar Daily Nigerian Malam Jaafar Jaafar ya tabbatarwa da kwamitin Majalisar dokokin jihar Kano cewar wannan faifan bidiyo da ya wallafa gaskiya ne.
A yayin da ya bayyana a gaban kwamitin Jaafar ya kare kambunsa na sahihancin faifan bidiyon da ya wallafa kan mai girma Gwamna yana karbar kudaden kasar waje daga hannun ‘Yan kwangila.
Cikin tsauraran matakan tsaro Jaafar ya bayyana a gaban zauren majalisar dokokin jihar Kano, bayan da jami’an tsaro suka yi masa rakiya daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano zuwa harabar Majalisar dokokin jihar Kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button