Labaran Duniya

Shugabannin kasashen duniya 10 da suka fi arziki a doron duniya

Ba sabon abu bane ba dai fitar da jerin sunayen mutane da suka yi fice a fannoni da dama na duniya kamar arziki da ma dai sauran su.

Sai dai ba kasafai ne ake sanin irin tarin arzikin da shugabannin kasashen duniya ke da su ba musamman hakan bai rasa nasaba da daman can wasun su masu kudi ne sannan kuma da kudin gwamnati suke yin dukkan hidindimun su.

Wasu kuma shugabannin sukan dade har ma wasu su mutu akan karagar mulki, don haka ne ma sanin hakikanin arzikin nasu yake da dan wuya.

To amma kamar kowa a duniya, suma shugabannin kasashe suna da nasu arzikin na kashin kansu wanda ba na gwamnati bane.

NAIJ.com dai ta tattaro maku wasu shugabannin kasashen da ake tunanin suna da tarin dukiya, kuma ga su kamar haka:

1. Vladimir Putin na kasar Rasha

2. Maha Vajiralongkorn na kasar Thailand

3. Hassanal Bolkiah na kasar Brunei

4. Khalifa Bin Zayed al Nahyan na kasar gamammiyar daular Larabawa (U.A.E)

5. Mohammed Bin Rashid mataimakin shugaban kasar gamammiyar daular Larabawa (U.A.E)

6. Donald Trump na kasar Amurka

7. Hans Adams Yarima mai jiran gado Liechtenstein

8. Mohammed na 6 na kasar Morocco

9. Sebastian Pinera

10. Salman bin Abdulaziz Al-Saud na kasar Saudiyya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button