Labaran siyasa

Shugaban Kasa Buhari Ya Mika Ragamar Jagorancin Yakin Neman Zabensa Ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Kasa Buhari Ya Mika Ragamar Jagorancin Yakin Neman Zabensa Ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Kasa Buhari Ya Mika Ragamar Jagorancin Yakin Neman Zabensa Ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.  
A yau Litinin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanarda mika ragamar yakin neman zaben shugaban kasa ga jigon jam’iyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, maimakon Shugaban kasa Buhari, yanzu Tinubu shine zai jagoranci yakin neman zaben da za’ayi a watan Feburairu. 
Shugaban kasa Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da yake kaddamar da Shugabancin yakin neman zaben 2019 a babban dakin taro na kasa da kasa dake Abuja. 
Kafun Shugaban kasa Buhari ya fitar da wannan sanarwa, Bola Tinubu da mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo sun kasance mataimaka ne ga shugaban kasa Buhari kamar yadda aka tsara shugabancin yakin neman zaben.
A cewar shugaban kasa Buhari, ya ragewa kansa nauyi ne saboda bayason dawainiyar siyasa ya wahalarda gudanarda gwamnati.
Tuni masana da masu fashin baki ke cigaba da tofa albarkacin bakinsu akan hakan, yayinda wasu ke ganin hakan bai dace ba, wasu kuma cewa suke. “Muddin Shugaban ya shiga fagen siyasa dumu-dumu, to gudanarda gwamnati kan iya samun nakasu saboda harkar ta siyasa, amma ragewa kansa nauyin da yayi zai bashi damar cigaba da ayyukan ofishin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button