Labarai

Shugaba Muhammadu Buhari zai sa hannu ga doka na baiwa Matasa Damar Tsayawa Takara

Kudirin dai zai baiwa matasa masu shekara 35 damar shiga takarar neman shugabancin kasar yayin da ya bai wa matasa masu shekara 30 damar neman gwamna.

Abun farin ciki ga matasa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa sanya hannu ga doka domin baiwa matsasa damar tsayawa takara.
Domin raya ranar dimokradiya, shugaban ya bayyana hakan ne a wajen jawabin sa safiyar ranar talata.

Tun a cikin watan juli na 2017 majalisar tarayya ta amince da kudirin tsayawa takarar shugabancin kasa da jiha da sauran kujerun siyasa na kasa.

Shugaban yana mai cewa “Nan da ‘yan kwanaki kadan zan sadu da matasa da dama na kasar nan domin sanya hannu kan kudurin dokar da za ta bai wa matasa damar tsayawa takara.”

Kudirin dai zai baiwa matasa masu shekara 35 damar shiga takarar neman shugabancin kasar yayin da ya bai wa matasa masu shekara 30 damar neman gwamna.

Haka zalika, kudurin ya amince ‘yan shekara 25 su tsaya takarar zama wakilai a majalisar wakilan kasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button