Kannywood

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin jaruman fina-finan Hausa maza da mata, hotuna

A daren ranar Alhamis, 18 ga watan Oktoba, ne jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood su ka ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa dake birnin tarayya, Abuja.

Jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood sun cika da murna da farinciki a yayin da su ka ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa domin nuna goyon bayansu gare shi.
Akwai annashuwa da fara’a a fuskokin jaruman, maza da mata, a hotunan da su ka dauka da shugaba Buhari yayin ziyarar.

Masana’antar Kannywood ta dade tana bawa shugaba Buhari goyon baya, don ko a shekarar 2015 bayan Buhari ya lashe zabe, kafin a rantsar da shi, sai da jaruman masana’antar ta Kannywood su ka kai masa ziyara a gidansa da ke Daura.
Daga cikin jarumana da su ka kaiwa shugaba Buhari wannan ziyara akwai; Hamisu Lamido (Iyantama), Daushe, Nura Hussain (Ya sayyadi), Rukayya Dawayya, Fati Nijar, Sadiq M. Sadiq, Aminu Saira, Rabi’u Rikadawa, Fati Shu’uma da wasu da dama.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button