Kiwon Lafiya

Shin ko kasan Amfanin Dabino a jikan dan Adam ?

Amfanin dabino wajen kiwon lafiya. hadisai da ingantattun bayanan tarihi sun bayyana yadda manzon tsira ( S.A.W) yake fadin alherin da ke tattare da dabino. Sau tari yakan fifita dabino, madara da zuma kan sauran abinciccikan yau da kullum.
    A matsayinsa na likitan likitoci, manzo (S.A.W) ya fi kowa kaifin basirar sanin abin da jikin dan adam yake bukata. Don haka, ko a zamanance an fitar cewa dabino na saurin narkar da abinci don samun saukin sarrafa shi zuwa ga sassan jikin dan adam.

Kwarai kuwa, dabino sinadari ne na musamman don warkar da dukkanin Cututtukan da mace zata gamu da su, ko na bayan haihuwa da sauransu. Wasu daga cikin amfanin dabinon har wa yau sun hada da:

✓ Yana Sanya kuzari yayin ibadar aure (tsakanin mata da miji).

✓ Yana taimakawa wajen karin jini.

✓ Yana maganin basir mai sa tsugunni a bayi.

✓ Yana Kara kaifin idanu da lafiyarsa.

✓ Yana rage nauyin kiba ko katon tumbi, wanda akafi sani da ‘Teba’.

✓ Yana maganin gudawa.

✓ Yana saurin saukar da hawan jini.

✓ Yana taimakawa kwakwalwa wajen samun basira.

✓ Yana kariya daga sihiri.

✓ Yana taimakawa mata masu ciki don samun sauki wajen haihuwa.

Ko Dabino na maganin Ciwon Nono Ga Mata?

Warkar Da Ciwon Nono.

Yadda za’ayi amfani da shi wajen warkar da ciwon nono ga wadda ta haihu kuwa shine a rika cin kwayar dabino guda bakwai (7), a Sha man tafarnuwa karamin cokali sau daya a rana har na tsawon kwanaki uku

Domin samun Ni’ima Ga Ma’aurata
Ana daka dabino a zuba cikin madara ‘Freesh milk’ sannan a saka zuma a ciki a Sha awa daya kafin saduwa.

Amfanin Dabino Ga Mata Masu Juna Biyu
Anacin dabino kwara bakwai kullun da safe idan an yi kusan haihuwa. Wannan yana hana wa mace yawan zubar jini lokacin haihuwa da iznin Allah.

Gudawa:
 Ana daka garin dabino a saka a ruwan zafi a sha insha’allah yana tsayar da gudawa.

Samun Kuzari:
 Ana cin dabino guda uku, a sha zuma cokali daya da safe da yamma.

Yadda Dabino Ke Gyara Fatar Jikin Mutun:
  Ana hada garin dabino da zuma da man zaitun a shafa a fuska, awa daya sai a wanke fuskar da ruwan zafi,
Wannan yana saurin gyara fuska. Bincike ya nuna yawaita cin dabino na hana kamuwa da ciwon daji wato ( Cancer) ko wacce iri.

Haka Kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce ‘Dabinon ajuwa yana maganin dukkan Cututtuka, kuma duk ranar da mutun ya ci irin wannan dabino na Ajuwa ( Wato Wanda ake tsinkowa daga birnin Madina, Wanda aka tabbatar a gonarsa ake samun dabinon), babu wata cuta da zata sameka a wannan rana ko sammu ko sihiri.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button