Labarai

Sheikh Ibrahim Khalil: Na raba gari da Gwamna Ganduje

Sheikh Ibrahim Khalil mai bai wa gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano a Najeriya shawara a kan ayyukan na musamman ya sanar da murabus daga mukaminsa.

Shaihin malamin ya fada wa wakilin BBC a Kano, Ibrahim Isa cewa bai bayyana dalilinsa na ajiye aikin ba, saboda yana son mutane su yi amfani da hankalinsu wajen gane nufinsa.
Amma ya ki amincewa da maganganun da ake yi cewa ya ajiye mukaminsa ne saboda zargin da ake wa gwamnan Kano da aikata laifukan ci hanci da rashawa.
Sheikh Khalil ya ki fada wa BBC ko zai bayyana dalilan nasa nan gaba.
Ya ce ba zai ce uffan ba ne saboda batun na gaban shari’a:
“Haramun ne malami yayi fatawa akan wata matsala da ke gaban alkali.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button