Magungunan Gargajiya

SHAN ZUMA DOMIN RAGE KIBA

Zuma na taimakawa wajen taso da sinadaran da suke sanya kiba, wadanda ke kwance a cikin jiki, tana fito da su ne don su bi jiki a lokacin da a ke aikin karfi, raguwarsu a jiki zai sanya kiba ta rage.
A lokacin da za a sha zumar ya kamata a gauraya zumar da ruwan zafi, sannan ana so idan har za a sha zumar, to a sha da sanyin safiya, idan an tashi sallar asuba ko kuma lokacin da aka farka daga barci.
Kuma idan aka gauraya zuma da ruwan zafi da kuma lemon tsami, sannan aka sha za su taimaka wajen rage kiba da kuma nauyin 
Jiki
CIN AYABA DOMIN RAGE KIBA.
SHAN ZUMA DOMIN RAGE KIBA
*******************************
Cin Ayaba guda 3 duk safiya kanfin Mutum yaci abinci haka ma da dare in za’a kwanta na matuqar rage kiba a wata daya zaka ga cenji a jikinka.
HADA KANKANA DA CITTA DOMIN RAGE KIBA
A samu kwallon kankana kamar guda biyu haka sai a markade su su zama ruwa a zuba garin citta, sai a dan sa ruwa sai a markada har sai yayi laushi Sai a ringa sha in rana ta yi zafi.
ABIN LURA ANAN
————————–
Yana da kyau a kula cewa kiba bata raguwa sai an rage cin abinci mai maiko sannan duk aka ci abincin rana kada a zauna a dan samu ayi wani aiki kona 15 mint ne

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button