Labarai

RUFE BODA YA KAWO WA NAJERIA DUMBUN ALHERI – Hameed Ali

RUFE BODA YA KAWO WA NAJERIA DUMBUN ALHERI – Hameed Ali

Hukumar fasa kwauri ta kasa ta bayyana cewa, babu shakka tana ganin ribar rufe bododi da shugaba Buhari yayi.
Shugaban Hukumar, kanal Hamid Ali mai Riyata, ya ce a cikin watan Satumba, akwai narar da suka sami kudaden shiga daya kai Naira Biliyan 9.2 a rana daya.
Ya kara da cewa, tun daga ranar da aka rufe Boda, daga Hukumar ta samu naira Biliyan 4.7 ko kuma ta samu Naira 5.8 a haka abin yake tafiya kullum.
Abin da na fuskanta, tun bayan rufe Bodar, yankin Kasar Benin, masu amfanin da wadancan barayin hanyoyin daga Janhuriyar Benin zuwa Najeriya, sun dawo gare mu Yanzu, in ji Hamid Ali.
Saboda Yanzu safara ta dawo ta cikin Ruwa kai tsaye, ko dai Tashar Apapa ko kuma Tsibirin Tinkan.
In dai za a ci gaba da rufe Bidodin nan, to tabbas za mu ci gaba da samar wa da kasa alheri, in ji shi.
Ko a bangaren harkar mai, wannan garkame Boda ya baiwa Hukumar mu, ceto mai Lita Miliyan 10.2 kullum da ake wofantar wa in ji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button