Labarin wasanni

Ronaldo ya amince ya biya harajin fam miliyan 16.6

Shahararren dan wasan kwallon kafa nan na Juventus Cristiano Ronaldo ya amince ya biya wata kotun birnin Madrid makudan kudade game da laifin kaucewa biyan haraji.
Tsohon dan wasan Real Madrid zai biya Yuro miliyan 18.8 (kimanin fam miliyan 16.6m).
Manema labarai sun gana da dan wasan a wajen kotun, bayan da alkalin kotun ya ki amincewa ya bayyana a bidiyo ko kuma ya shiga ginin da mota don kaucewa cincirindon jama’a.
Yarjejeniyar, wadda aka cimma ta hada da daurin wata 23.
Amma a kasar Spaniya masu laifi ba kasafai suke yin zaman gidan yari ba a hukuncin da bai kai shekaru biyu ba.
Abu ne mawuyaci Ronaldo ya zauna a gidan yari duba da irin laifin da ya aikata, saidai ta hanyar gyara-halinka.
Wani dan jarida Ruben Canizares ya wallafa wani bidiyon dan wasan yayin da ya isa kotun tare da budurwarsa Georgina Rodriguez.
Laifin da ake zargin Ronaldo
Dan wasan, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau biyar, ana zarginsa ne da kauce wa biyan haraji tsakanin shekarar 2010 zuwa 2014 a lokacin da yake wa Real Madird wasa.
Ronaldo ya amsa laifuka hudu wadanda suka kai Yuro miliyan 5.7 kamar yadda wani kamfanin dillancin labarai ya ruwaito a Spaniya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button