Labarai

RIKICIN KADUNA: An dakatar da tura ’yan Bautar kasa (NYSC) zuwa Kaduna

Hukumar Kula da Ayyukan Bautar Kasa (NYSC), ta bayar da sanarwar dakatar da tura matasa masu yi wa kasa hidima na ‘Batch C’ na 2018, zuwa aikin bautar kasa a jihar Kaduna.
An fitar da wannan sanarwa a yau Litinin biyo bayan rikicin da ya barke jiya Lahadi, wanda ya yi sanadiyyar kafa dokar hana shiga Kaduna ta awa 24.
Rikicin dai ya samo asali ne daga fadan da ya farke a Kasuwar Magani a ranar Alhamis da ta gabata, wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane 55 kamar yadda hukumar ‘yan sanda ta tabbatar.
Gobe Talata ne 23 Ga Oktoba, ya kamata masu yi wa kasa hidimar su isa Kaduna, amma an umarci kowa ya zauna a gida har sai ya ji sanarwa ta gaba.
Daga su ma ‘yan sanda sun umarci matafiya da sauran masu ababen hawa kada su bi cikin Kaduna, su wata hanyar da za su bi su iya garuruwan da suka dosa.
’Yan sanda sun ce kada matafiya su bi ta Kaduna
Biyo bayan rikicin da ya barke a cikin garin Kaduna da ya yi sandiyyar kafa dokar ba shiga ba fita a Kaduna da kewaye, hukumar ‘yan sanda ta umarci matafiya da kada su shigo kuma kada bi ta Kaduna.
Dangane da haka, an umarci masu ababen hawa da su nemi wata hanyar da za su iya bi su tafi garuruwan da suka dosa.
Kakakin ’Yan sanda na Kasa, Jimoh Moshood ne ya bayyana haka a cikin hirar da aka yi da shi Gidan Talbijin na Channels, da safiyar yau Litinin.
Ya kara da cewa akwai hanyoyin da matafiya za su iya bi domin su kewaye wa shiga cikin Kaduna. Don haka mu na shawartar masu ‘yan uwa da abokan arziki da ke da niyyar yin tafiya, su sanar da su cewa kada bi ta Kaduna, su nemi wata hanyar da su iya bi su bulla garuruwan da za su tafi.
Sai dai kuma ya kara da cewa an shirya kyakkyawan tsaro ga wadanda za su tafi Abuja zuwa Kaduna, da kuma masu tafiya zuwa Kaduna ta cikin jirgin kasa.
Ya ce da zarar an ga komai ya lafa sosai, to za a rage zangon dokar hana walwalar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button