Labaran Duniya

Rikici a jihar Plateau ya yi sanadin salwantar rayuka

A kalla mutum 20 ne suka mutu a wani hari da aka kai a kauyen Ancha dake jihar Filato a yankin tsakiyar Najeriya.
Haka kuma wasu da dama sun jikkata a harin da aka kai kauyen da ke gundumar Bassa a cikin daren Alhamis.
Mazauna kauyen sun zargi makiyaya da cewa sune suka kai harin don ramuwa ga wani kisa da aka yi a makon da ya gabata.
Dama dai ana yawan samun rikice-rikice a jihar Filato tsakanin Musulmai wadanda sune mafi yawa a arewacin jihar da kuma Kiristoci da suka fi yawa a kudancinta.
Wadansu mahara ne suka kai wannan harin a cikin daren jiya da bindigogi da adduna, kamar yadda mazauna kauyen wadanda suka tsere zuwa cikin daji domin ceton rayukansu.
Daga baya maharan sun gudu.
Nigeria: ‘Yadda muka kama masu ‘safarar jarirai’ a Jos’
Mahara sun kashe basarake a Jos
An kashe mutane 14 a kauyen Jos
Rahotanni daga yankin suna cewa wata rundunar ‘yan sanda da sojoji sun tafi kauyen daga baya domin duba irin barnar aka yi, kuma su gano wadanda suka kitsa wannan rikicin.
Wannan harin da aka kai wa al’umomin wannan kauyen dake kimanin kilomita 40 yamma da birnin Jos ya zo wa yawancin jama’a da mamaki saboda yadda yankin ya soma samun zaman lafiya, musamman a cikin shekaru biyu da suka gabata.
A da, wannan jihar ta sha samun aukuwar tashe-tashen hankali da rikicin kabilanci da na addini da suka hada da rikicin makiyaya da manoma.
Najeriya na fuskantar kalubalen rashin tsaro wadanda suka hada da na Boko Haram a arewacin kasar da kuma satar mutane domin kudin fansa a sauran sassan kasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button