Labaran wasanni

Real Madrid Za Ta Nemi Harry Kane A Kakar Wasa Mai ZuwaKungiyar kwallin kafa ta Real Madrid ta zabi dan wasan Tottenham, Harry Kane a matsayin wanda zai iya maye gurbin Karim Benzema a Santiago Bernebeu kamar yadda wasu jaridu suka ruwaito a kasar ta Sipaniya. 
Kungiyar dai tana fama da rashin zura kwallo a raga sakamakon rashin kokarin da dan wasan gaba na kungiyar yake wato Gareth Bale.
 A kakar wasan data gabata ne kungiyar ta siyar da dan wasanta na gaba Albaro Morata zuwa Chelsea ta kasar ingila wanda hakan yasa magoya bayan kungiyar suke ganin hukuncin baiyi daidai ba. 
Tuni dai kungiyar ta fitar da yan wasa irinsu Kylian Mbappe da Harry Kane a matsayin wadanda za su maye gurbin Benzema wanda ake tunanin zai bar kungiyar zuwa Arsenal ta kasar ingila.

Harry Kane dai a yan kwanakin nan yaja hankalin kunyoyi irinsu Manchester United da PSG da Jubentus da Barcelona da kuma Real Madrid din. Ya kuma yazura kwallaye dayawa a wannan kakar ciki har da kwallo biyu daya zura a ragar Liverpool a makonni biyu da suka gabata a gasar firimiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button