Labaran wasanni

Real Madrid Ne Suka Daina Ganin Girmana Shi Ya Sa Na Tafi -Ronaldo

Cristiano Ronaldo ya ce babban dalilinsa na rabuwa da Real Madrid zuwa kungiyar Jubentus shi ne fahimtar da yayi cewa, shugaban kungiyar ta Real Madrid Florentino Perez ba ya ganin kimarsa, kamar yadda yake yi a baya.
Ronaldo ya bayyana haka ne a ganawar da yayi da wata mujallar wasanni ta kasar Faransa, inda ya kara da cewa, bayaga shugaban na Real Madrid wasu daga cikin mambobin kungiyar ma sun daina daukarsa da muhimmanci.
Ronaldo ya ce, ya soma fuskantar rashin bashi kima a Real Madrid bayan shafe shekaru 5 da komawa cikinta bayan rabuwa da tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United.
Yayin hirarsa da Mujallar wasannin, dan wasan na Jubentus ya kara da cewa ajiye aikin horar da Real Madrid da mai horar da shi Zinaden Zidane yayi, ya kara masa kwarin gwiwar rabuwa da kungiyar, domin gwada sa’arsa a wata.
A watan Yulin da ya gabata Ronaldo ya koma Jubentus kan kudi yuro miliyan 100, bayan shafe shekaru 9 yana hasakawa a Real Madrid inda yaci kwallaye 450 cikin wasanni 438.
Tun bayan zartas da matakin rabuwa da Real Madrid da Cristiano Ronaldo yayi, har yanzu kungiyar ta gaza samun dan wasan da zai maye gurbinsa wajen ci mata kwallaye a wasannin da take fafatawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button