Labaran wasanni

PSG na Zawarcin De Gea

Kungiyar kwallon kafa ta PSG tana zawarcin mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Dabid De Gea domin ya koma kungiyar a kakar wasa mai zuwa kamar yadda rahotanni suka bayyana. 

Dan wasan dai yana shekara ta takwas a kungiyar Manchester Unitted tun bayan daya koma kungiyar daga kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid dake kasar Sipaniya. 

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United dai tana son dan wasan yaci gaba da zaman kungiyar bayan data yimasa tayin sabon kwantaragi sai dai dan wasan baya son zaman kungiyar indai kociyan kungiyar Jose Mourinho zaici gaba da zama. 

Hakan yasa kungiyar kwallon kafa ta PSG tafara zawarcin mai tsaron ragar domin ya maye mata gurbin Gianluigi Buffon wanda ya koma kungiyar daga kungiyar kwallon kafa ta Jubentus din kasar Italiya. 

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai tad ade tana zawarcin mai tsaron ragar wanda a shekara ta 2015 ya kusa komawa kungiyar kafin  a samu matsalar na’urar aika sako.

De Gea dai ya buga wasanni da dama a kungiyar Manchester United yayinda kuma ya buga wasanni da dama a tawagar ‘yan wasan kasar Sipaniya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button