Labaran wasanni

Nijeriya Ta Gayyaci Ahmad Musa Da Dan Wasan Kano Pillars Lokosa

Mai koyar da tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nijeriya, Gernot Rohr, ya bayyana sunayen ‘yan wasa 23 da zasu wakilci kasar nan a wasannin da kasar za ta buga da kasar Africa ta kudu da kuma Uganda a wata mai kamawa.
Acikin ‘yan wasan da kociyan ya gayyata akwai wadanda daman suna wakiltar kasar nan a wasanni daban daban akwai kuma wadanda basu taba bugawa kasar nan wasa ba sai a wanann lokacin.
Dan wasa mai kokari Aled Iwobi na Arsenal da kuma Idion Ighalo sune ‘yan wasan gaba da zasuja ragamar ‘yan wasan na Nijeriya sai kuma matashin dan wasa Samuel Chukwenze na kungiyar Billareal ta kasar Sipaniya.
Dan wasa Ahmad Musa a wannan lokacin ma shi ne zai zama kyaftin din tawagar ‘yan wasan sakamakon har yanzu dan wasa Mikel Obi na kungiyar TianjinTeda bai gama warkewa ba tun bayan kammala gasar cin kofin duniya rabonsa da yayiwa Nijeriya wasa,
Nijeriya dai itace take jan ragamar rukuni na E da maki tara sai Africa ta kudu a matsayi na biyu da maki bakwai yayinda kasashen biyu zasu kece raini a ranar 17 ga watan gobe a kasar Africa ta kudu.
Ga Jerin ‘Yan Wasan Da Aka Gayyata
Masu Tsaron Raga: Ikechukwu Ezenwa, Daniel Akpeyi, Francis Uzoho
‘Yan Wasan Baya: William Troost-Ekong, Leon Balogun, Kenneth Omeruo, Brian Idowu, Olamilekan Adeleye, Semi Ajayi, Jamilu Collins, Ola Aina.
‘Yan Wasan Tsakiya: John Ogu, Mikel Agu, Oghenekaro Etebo.
‘Yan Wasan Gaba: Odion Ighalo, Ahmed Musa, Bictor Osimhen, Aled Iwobi, Kelechi Iheanacho, Samuel Kalu, Isaac Success, Moses Simon, Samuel Chukwueze.
Masu Jiran Ko Ta Kwana: Henry Onyekuru, Chidozie Awaziem, Sunday Adetunji, Nyima Nwagua, Junior Lokosa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button