Kannywood

Nida fim din Hausa mutu ka raba -Jamila Nagudu

Jamila Umar Nagudu jaruma ce wacce samun wata jarumarda zata kara da ita abu ne mai kamar wuya saboda yadda ta iya taka rawa a fannoni dayawa na shirye shiryen Kannywood.

Jamila ta jima acikin masana’antar fim kuma tana cikin wadanda suka mori zamaninsu a masana’antar musamman idan aka duba yadda tauraruwarta ke haskawa tun shigowarta har rana mai kamar yau. Sannan kuma tana daga cikin jarumai mata da suka samu manyan kudade karkashin sana’ar fim bayan kudaden tallace tallacen kamfanoni Nigeria dama wasu kasashen makwabta da take samu.

Auren jamila ya jima da mutuwa tun lokacinda take mahaifarta a jihar Bauchi kuma bata taba labartawa koda ‘yan jaridu cewa zata sake wani auren ba saidai watakila kodan kafuwarta a masana’antar ne yasa take ganin idan ta bari damarda take daita zata kubuce.

Rashin auren jamila nagudu yana kada hanjin wasu daga masoyanta wadanda suke burin ganin ta sake aure saidai kuma watakila ita ta hango wani abinda basu hango ba acikin komawa rayuwar aure gareta.

Jamila Nagudu tanada yara wadanda ta kafa dayawa acikin masana’antar Kannywood tun daga kan daraktoci, furodusoshi dama jarumai mata da maza wadanda sukaci albarkacinta.

Jarumai mata dayawa a kannywood sun cirewa kansu zancen aure saboda yadda mazaje ke aurensu don bukata kawai daga baya a sakesu. Wannan shine babban kalubale dayake addabar mata masu shigowa masana’antar fina finai.

Source: Hausaline

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button