Labarai

Ni Na Jagoranci Bada Cin Hancin Dala Miliyan Biyar Ga Ganduje – Dan Kwangila

Arewa Daily Post ta ruwaito wani daga cikin ‘yan kwangilar da ya nemi a boye sunan sa ya fadi cewa tabbas shine ya rika mika wa Ganduje wadannan kudade kuma ya tona asirin sa ne don a gyara.

” Ni ban tona wa Ganduje asiri don son rai. Idan da haka ne da na yi amfani da bidiyon da na dauka muna biyan sa cin hanci sun fi 10 wajen azurta kaina ko kuma tilasta masa ya biya kamfanin mu kudaden da muke bin su.

” Ina da yakinin cewa idan ana fallasa jami’an gwamnati haka Najeriya za ta gyaru.

Gwamnatin jihar Kano ta karyata wannan bidiyo sannan ta ce tabbas za tu gudanar da bincike akai da idan ya kai ga a shiga kotu ne ma za a shiga don a wanke gwamna Ganduje.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button