Labaran siyasa

Ni ban san matsayin Tinubu a jam’iyyar APC ba – Obasanjo

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu cewa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa kawowa yanzu ba ya da masaniya kan matsayi na mukami da Asiwaju Bola ke rike da shi a jam’iyyar APC.

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin wani shirin mai taken “The Talk” da ake watsawa a tashar You Tube ta Voice of the People, watau Muryar Al’umma. A yayin wannan shiri tsohon shugaban ksar na amsa tamboyin dangane da mukaman wasu jiga-jigan ‘yan siyasa na kasar nan, inda ya bayyana Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya da kuma Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin mataimakin shugaban kasar. Ya kuma bayyana mukamin Sanata Abubakar Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawa ta Najeriya.

A yayin tuntubarsa dangane da mukamin tsohon gwamnan na jihar Legas, Obasanjo ya bayyana cewa, a halin yanzu ba ya da masaniyar wani mukami da Tinubu ke rike da shi a kasar nan ballantana kuma a jam’iyyarsa ta APC.

Yayin ganawarsa a cikin shirin na The Talk, tsohon shugaban kasar ya kuma sake jaddada goyon bayan sa ga dan takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, inda ya ce ya yi burin ya ci gajiyar kujerarsa ta shugaban kasa tun a 2007 sai dai rabo da bai tsaga da shi ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button