Labaran siyasa

Nasarorin da jam’iyyarmu ta samu a baya-bayan nan ya nuna cewa zamuyi nasara a 2019 – Buhari

– Shugaba Buhari yace jam’iyyar APC ce zata lashe zabukan 2019

Nasarorin da jam’iyyarmu ta samu a baya-bayan nan ya nuna cewa zamuyi nasara a 2019 - Buhari

– Ya ce zabukan cike gurbi da akayi kwanan nan alamu ne dake nuni ga hakan

– Yayi alkawarin ci gaba da iya bakin kokarinsa wajen ganin ci gaban Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya bayyana cewa nasarorin da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu a zabukan cike gurbi a Katsina, Bauchi da Kogi sun nuna cewa jam’iyyar ce zata lashe zabe a 2019.

Buhari ya bayyana hakan yayinda ya karbi bakuncin wakilan shugabanni 34 na kungiyar kananan hukumomin Najeriya a jihar Katsina.

Nasarorin da jam’iyyarmu ta samu a baya-bayan nan ya nuna cewa zamuyi nasara a 2019 – Buhari
Ya mayar da hankali sosai a nasaroron zabukan baya-bayan nan cewa tabbass alamu ne na abubuwa masu zuwa.

Ya godema shugabannin kungiyar kan ziyarar Sallah da suka kai masa tare da sakon taya murna akan kokarin jam’iyyar da gwamnatinsa, ya basu tabbacin cewa zai ci gaba da yin iya bakin kokarinsa ga kasar.

Da yake magana a madadin mambobin kungiyar shugaban ALGON a jihar, Alhaji Mohammed Na’Allah ya nuna goyon bayansu da jajircewarsu wajen ganin nasarar gwamnatin Buhari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button