Labaran siyasa

Najeriya Na Iya Cigaba Da Zama Hedikwatar Talaucin Duniya –Sarkin KanoSarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi na biyu, ya ce tabbas in hukumomi basu dauki matakan da suka dace wajen gyara tattalin arzikin kasar nan ba, to Nijeriya za ta ci gaba da zama a matsayin babban birnin talauci da fatara ta duniya zuwa lokaci mai tsawo, tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya ya fadi hakan ne a wani taro da aka gudanar a Jami’ar Ibadan, inda aka karrama shi da lambar girma. 

‘In duk kasashe suka ci gaba akan yadda suke tsara tattalin arzikinsu yanzu, har zuwa shekarar 2050 to kashi 80 cikin 100 na matalauta zasu fito ne daga kasashen Afirika, wannan bashi bane abinda ya fi tada hankali, fiye da rabi na wannan adadin matalauta kashi 80 din zai fito ne daga kasashen Nijeriya da Jamhuriyyar Kongo, wato wadannan kasashen biyu zasu samar da adadin matalauta kashi 40 cikin 100 kenan, don haka Nijeriyar za ta ci gaba da zama babban birnin talauci na duniya.’ Inji Sanusi.

Sanusi ya ci gaba da cewa: Kasar nan tana da albarkar manyan mutane, kasar da ta ke da manyan Farfesoshi, manyan masana da masu ilimi, a shekarar 1960 kudin shigar Nijeriya yafi na Koriya ta kudu da kasar Sin, mahaifi na ne jakadan Nijeriya na farko a kasar Sin a shekarar 1972, a wannan lokacin duk makonni biyu sai ya je Singafo don siyan kayan masarufi saboda babu su a birnin Beijin na Sin din a wannan lokacin, hatta abubuwa irinsu madara, sukar da gurguru babu a Beijin.

Bana bukatar jin yadda mutane suke maganar karamomi irin na da din nan, jama’ar kasar Sin mutane masu jini da tsoka kamar mu, amma gashi sun ciyar da kasar su gab aba tare da sun jira wata karama ta faru ba, rashin tsare-tsare masu kyau da suka dace ne yake damun kasar mu, yanzu gashi zaben shekarar 2019 ya gabato, ina karantawa kullum a labarai, amma abun mamaki babu mai maganar zai gyara ilimi daga cikin ‘yan siyasar nan, bas a maganar yadda zasu ciyar da al’umma, ba batun gyara harkar kiwon lafiya, amma suna maganar yadda za a kashe kudaden rarar man fetur har kusan Tiriliyan 2, ina hankalinmu da tunanin abinda ya dace yake?’ inji Sanusi

 A karshe Sarki Sanusi yana cewa: Ya rage garemu da muke da tunanin makoma mai kyau ga kasar mu, in har bama so mu zama babban birnin fatara na duniya, to muna da shekaru 30 a gaban mu, yanzu zamu fara aiki kafin lokaci ya kure mana, yakamata mu hangi kasashe irinsu Taiwan, Sin, Singafo, da yadda suka ci gaba, basu dogara da albarkatun man fetur ko zinare ba wajen ciyar da kasar su gaba, mu dauke su a matsayin misali babba gare mu wajen tashi tsaye da tabbatar da ganin mun kawo karshen wannan babbar barazana ta fatara da muke fuskanta, mu yi ko saboda ‘ya’ya da jikokinmu masu tasowa.

source: leadershipyau.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button