Labaran wasanni

Na shiga damuwa lokacin Da Mourinho yana United – Pogba

Dan kwallon Man United, Paul Pogba ya ce ya shiga damuwa, bayan da ya samu rashin jituwa da Jose Mourinho a lokacin da yake koch a Old Trafford.

Dangantaka tayi tsami tsakanin dan wasan, mai shekara 29 da Mourinho, wanda ya karbe mukamin mataimakin kaftin dafa wajen Pogba.

To sai dai kuma a cikin watan Disambar 2018, United ta kori Mourinho.

”Na shiga hali na damuwa karo da dama a sana’ar tamaula da nake yi, sai dai ba za ka tattauna kan batun ba.

”Wasu lokacin, ba za ka san kana cikin damuwa ba, kawai za kaji ba ka son shiga mutane, kuma ba ka son yin magana da kowa.

”Ni kaina na fara shiga wannan yanayin a lokacin da Mourinho ke kocin Manchester Unted. Sai ka tambayi kanka kaine kakae da laifi, saboda ba ka taba samun kanka cikin wannan yanayin ba a rayuwa.”

Pogba ya koma United da taka leda kan fam miliyan 89 a matakin wanda aka saya mafi tsada a duniya a shekarar 2016, kuma lokacin Mourinho ya maye gurbin Louis van Gaal a kakar gaba.

Mourinho ya lashe League Cup da Europa League a shekarar 2017 tare da United, daga baya dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da ‘yan wasu ‘yan wasa da mahukuntan kungiyar.

cc bbc hausa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button